An daure wanda ya kai wa Raheem Sterling Hari

Raheem Sterling na Manchester City Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Raheem Sterling shi ne ya fi ci wa Manchester City kwallo a bana

An daure wani tsohon mai laifi da ke tayar da zaune tsaye a wajen wasan kwallon kafa a kan laifin cin mutunci da kai harin wariyar launin fata kan dan wasan Manchester City da Ingila Raheem Sterling.

Karl Anderson, mai shekara 29 ya amsa laifinsa na kai hari a kan Sterling saboda bambancin launin fata a kofar filin atisaye na Manchester City a ranar Asabar.

Masu gabatar da kara sun sheda wa kotun cewa Anderson yana da tarihin aikata laifuka, inda aka taba yanke masa hukunci sau 25 na laifuka 37, ciki har da wadanda suka shafi wasan kwallon kafa.

A yanzu dai an yanke masa hukuncin zaman gidan yari na mako 16, kuma zai biya diyyar fam 100.

Anderson wanda ya doki Sterling sau hudu a lokacin harin, ya ce ransa ya baci ne, amma yana nadamar abin da ya yi.

Mutumin ya kuma zagi Sterling zagi irin na wariyar launin fata tare da ce masa, yana son ya ga matar dan wasan da dansa sun mutu.

A bahasin Sterling mai shekara 23 na illar abin da aka yi masa, wanda aka karanta a kotun ya ce, bai taba tunanin irin wannan halayya za ta faru a kasar ba a wannan rana da kuma shekara.

Hoton bidiyon kyamarar tsaro da ke kofar filin wasan wanda aka nuna a kotu kan yadda abin ya faru, ya nuna yadda mutumin ya tsaya da motarsa a kusa da Sterling.