Zakarun Masar sun yanka sa domin samun sa'a

Lokacin yanka san Hakkin mallakar hoto Tarek Talaat
Image caption Bayan yanka san sai 'yan wasan kungiyar suka ba wa talakawa sadakar naman

Sakamakon doke su da aka yi a wasa daya suka kuma yi canjaras a wani, ma'aikata da 'yan wasan kungiyar Al Ahly ta Masar sun yanka sa, sannan suka yi sadaka da naman ga talakawa domin sa'arsu ta farfado.

Zakarun na Masar sun gamu da rashin sa'a a karon farko a gasar Premier ta kasar tun a watan Yuni na 2016, lokacin da suka sha kashi da ci 3-2 a gidan Misr Al Makassa a farkon watan nan.

Bayan rashin nasarar a wancan lokacin, a ranar Juma'a da ta wuce ne kuma suka yi canjaras 1-1 da mai masaukinsu Tanta.

A yanzu kungiyar ta Al Ahly ita ce ta uku a teburin gasar Premier Masar bayan wasa 11.

Maki hudu ne tsakaninsu da ta daya a teburin Ismaili, wadda ta yi wasa 13 ya zuwa yanzu.

Labarai masu alaka