Afirka ta Kudu: Ana son kara shekarun da matasa za su sha giya da taba

Tarin barasa a wani kanti a Afirka ta Kudu Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shan barasa babbar matsala ce da ke addabar Afrika ta Kudu.

Wata babbar kungiyar dalibai a Afirka ta Kudu ta bukaci da a kara ka'idar yawan shekarun da doka ta amince matasa su sha taba da giya daga shekara 18 zuwa 21.

A wata sanarwa da kungiyar ta Congress of South African Students (Cosas) ta fitar wadda aka watsa ta shafin intanet na Times Live, ta ce abubuwan guda biyu suna kawo cikas ga matasa su cimma burinsu na samun nasara a fannin ilimin boko.

Sannan kuma abubuwan suna sanya dalibai matasa su yi watsi da makaranta.

A sanarwar kungiyar ta bukaci da rika hukunta duk matashin da yake kasa da shekara 21 da aka samu yana ta'ammali da taba ko barasa a gurfanar da shi a gaban kotu tare da yanke masa hukunci mai tsanani.

Kungiyar ta ce duk matashin da ke kasa da wadannan shekaru da yake shan abubuwan biyu yana neman watsa ci gaban Afirka ta Kudu ne kawai saboda haka bai kamata a kyale shi ba ba tare da hukunci ba.

Shan barasa babbar matsala ce da ke addabar kasar ta Afrika ta Kudu.

Labarai masu alaka