Nigeria: Sabon rikici ya barke a jam'iyyar PDP

PDP Nigeria Hakkin mallakar hoto PDP Twitter
Image caption Uche Secondus ya kayar da abokan takararsa uku a babban taron PDP

Rikici ya sake barkewa a babbar jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya, mako guda bayan zaben sabbin shugabanninta.

Sabon bangare na jam'iyyar karkashin jagorancin Emmanuel Nwosu ya bukaci a soke sakamakon zaben babban taron jam'iyyar da aka gudanar a ranar 9 ga watan nan a Abuja.

Sun yi zargin cewa an yi magudi da tafka kurakurai a tsarin zaben jam'iyyar.

Sannan sun zargi wasu gwamnonin PDP da yin kane-kane a harkokin jam'iyyar domin dora 'yan takararsu.

Zuwa yanzu babu wani martani da ya fito daga uwar jam'iyyar game da sabuwar dambarwar da ta barke.

Tun da farko dambarwa ta kunno kai ne bayan da wasu suka yi zargin an shirya magudi a babban taron, musamman bayan da wata takarda kafin a fara jefa kuri'a ta rika zagayawa hannun mahalarta taron dauke da jerin sunayen wasu 'yan takara.

Sabon rikicin na PDP na zuwa ne a yayin da jam'iyyar ke kokarin dinke barakarta domin kwace mulki daga hannun jam'iyyar APC mai mulki a zaben 2019.

Wasu masharhanta siyasar Najeriya na ganin rikicin jam'iyyar musamman kafin kaddamar da yakin neman zabe zai iya yin tasiri ga makokmarta a zaben 2019.

Jam'iyyar PDP da ta shafe shekaru 16 tana mulki a Najeriya, ta shiga rudanin shugabanci tun lokacin da ta sha kaye a zaben shugaban kasa da aka gudanar a 2015.