Swansea ta raba gari da kocinta Paul Clement

Paul Clement ya shafe wata shida yana jagorantar kungiyar Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Paul Clement ya shafe wata shida yana jagorantar kungiyar

Swansea City ta raba gari da kocinta Paul Clement bayan da ya shafe wata shida yana jagorantar kungiyar.

Swansea ce ta karshen baya a teburin firimiya, bayan da ta yi nasara a wasa uku kacal cikin wasannin da ta fafata a bana.

Clement mai shekara 45, ya karbi aikin kungiyar a watan Janairu a lokacin da kulob din yake cikin ukun karshen teburi, inda ya taimaka wa kungiyar ta kare a ta 15.

Har ila yau kungiyar ta bayar da sanarwar cewa mataimakan kocin Nigel Gibbs da Karl Halabi sun bar kulob din.

Kungiyar ta ce za kuma su bayyana sunan sabon wanda zai ja ragamar kungiyar "cikin sa'a 24 masu zuwa".

Kafin Clement ya koma Swansea, shi ne mataimakin koci Carlo Ancelotti a Chelsea da Paris St-Germain da kuma Real Madrid.

Labarai masu alaka