Kamfanin Apple yana rage karfin tsofaffin iPhones da gangan

iPhone user Hakkin mallakar hoto Getty Images

Kamfanin Apple ya tabbatar wa masu wayoyin iPhone cewa yana rage saurin wasu tsofaffin wayoyin na iPhone da gangan.

Masu hulda da kamfanin sun dade suna tuhumar kamfanin Apple din da rage wa tsofaffin wayoyin hannu na iPhone sauri domin a tilasta musu sayen sababbin wayoyin da suka fito.

Kamfanin ya fito fili ya bayyana cewa lallai yana rage wa wasu wayoyin sauri domin karfin batirin wayoyin na raguwa bayan wasu shekaru.

Apple ya ce yana yin haka ne domin ya "tsawaita ran" na'urorin da yake kerawa.

Lamarin ya fara bayyana ne a lokacin da wani mai amfani da wayar Iphone ya wallafa rahoton wani gwaji da ya yi a shafin intanet na Reddit, a inda ya nuna cewa wayarsa samfurin iPhone 6S ta rage sauri matuka amma ta fara saurin sosai bayan da ya sauya tsohon batirin da sabo.

"Na yi amfani da wayar dan uwana samfurin iPhone 6 Plus, kuma na lura wayar tasa ta fi tawa sauri.

"A lokacin ne na tabbatar cewa akwai lauje cikin nadi," inji mawallafin rahoton mai suna TeckFire.

Daga nan ne shafin fasahar yanar gizo, Geekbench ya binciki samfurin wayoyin iPhone masu amfani da manhajar iOS daban-daban, inda ya gano cewa lallai kuwa ana rage musu sauri da gangan.

Menene martanin da Apple ya mayar?

"Batiran na lithium-ion na rage bayar da karfin wuta a lokutan sanyi idan sun fara tsufa, wanda ya kan sa na'urar ta rika kashe kanta domin kare wasu sassa na wayar daga samun matsala," in ji kamfanin.

"A bara mun fitar da wani sabon tsari a iPhone 6S da iPhone SE domin rage matsalar mutuwar wayar a lokuta irin wadannan."

"A halin yanzu mun saka wa iPhone 7 mai manhajar iOS 11.2 wannan tsarin, kuma muna son saka wa sauran na'urorinmu a shekaru masu zuwa."

"Nufinmu shi ne mu samar wa masu hulda da mu tsarin mafi burgewa."

Me yasa baturan lithium-ion ke rage karfi?

Batiran Lithium na rage karfi bayan wani lokaci domin abubuwan dake faruwa a lokutan da ake cajinsu.

A lokutan caji da amfani da batiran lithium, wasu kwayoyin halitta masu sunan lithium ions na ratsa kayan da suka hada batirin.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Batiran lithium na rage karfi idan sun fara tsufa

Binciken da aka gudanar ya na cewa a duk lokacin da wannan ya auku, a kan sami wani sauyi ga tsarin batirin.

Wannan sauyin ya kan sa batirin ya rika sudewa, lamarin da kan hana shi rike caji kamar yadda ya saba a lokacin yana sabo.

Ko ya kamata da Apple ta sanar da abokan huldarta?

"Hanyar da kamfanin Apple ya bi wajen aiwatar da wannan tsarin shi ne ya kawo zargin da ake yi masa na rashin gaskiya," in ji Nick Heer, wani masanin fasahar manhaja.

"Kamfanin Apple ya dade yana gamsar da masu hulda da shi... wannan lokaci ne da suka baras da garinsu. Haka kawai, a ganina."

Sauya tsohon batirin iPhone na irin wannan wayar domin ta koma tana sauri kamar da na da tsada. Akan kashe kimanin fam 79 a Ingila, a Amurka kuwa ya kan kai dala 59, watau kimanin Naira 21,400.

"Ya kamata da sun fito fili game da batun tun baya," in ji Chris Green na kamfanin bincike na Bright Bee.

"Amma na san dalilin da ya sa suka yi haka. Saka wa wayoyin wannan tsarin na taimakawa wajen tsawaita ran na'urorin."

Labarai masu alaka

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba