Yadda zawarawa ke fuskantar matsi a cikin al'umma
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Adikon Zamani: Yadda zawarawa ke fuskantar matsi a cikin al'umma

Latsa alamar lasifikar da ke sama don jin ganawar da aka yi da wadansu zawara kan batun.

Adikon Zamani tare da Fatima Zahra Umar

Ana iya cewa abu mafi muni da ka iya faruwa a wajen mace a yankin arewacin Najeriya shi ne ta zama bazawara.

Ana kallon mata zawarawa a yankin matsayin wadanda ba su da daraja.

Ko kuma wadanda ba su da kima muddin suna amsa sunan zawarawa.

Irin wadannan matan sau da yawa ana takura musu da tsangwama da kuma gulmace-gulmace.

Bazawara a kasar Hausa ba ta da wani aji da ake saka ta a cikin al'umma, tun da ta wuce a kirata budurwa kuma ita ba matar aure ba ce.

Bazawara na tsakankanin wani gurbi mai hadari a tsakanin 'yan matanci da kuma zaman aure, wanda aka fi sani da "zawarci".

Kasancewar mace bazawara ba wai wulakanci kawai yake jawo wa mace a cikin al'umma ba a arewacin Najeriya, har da haifar da matsala a bangaren abin batarwa na yau da kullum.

Domin kuwa hakan ba karamar barazana ba ce, domin kuwa ba kowacce mace ba ce take da halin daukar dawainiyar kanta.

A wannan makon filin Adikon Zamani ya tattauna da wasu zawarawa da suka fada irin wannan hali.

Wadannan zawarawa na fuskantar wulakanci da muzgunawa a cikin al'umma, kuma suna yin iya kokarinsu don ganin sun fita daga cikin wanann halin.

Mun tambaye su wane irin hali da nuna wariya zawarawa suke fuskanta a cikin al'umma, da kuma yadda maza suke ci gaba da yin saki ba tare da kwakkwaran dalili ba.