Hotunan abubuwan da suka faru a Afirka a makon nan 18-22 Disamba

Zababbun hotunan wasu abubuwan da suka wakana a kasashen Afirka a makon nan.

A South African diver dressed as Santa Claus feeds a stingray as he swims in an aquarium during a show before Christmas at Africa's largest marine theme park, uShaka Sea World, in Durban on December 19, 2017. Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wani mai daka tsari da ya yi shiga irin ta Santa Claus yana bai wa kifi abinci a lokacin bikin shiga ruwa ranar Talata a birnin Durban na Afirka ta Kudu.
Egyptian Handicapped Mohamed Azeema (C) in action during the first disabled soccer match in Cairo, Egypt, 16 December 2017 Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Kungiyar kwallon kafar mutanen da aka yanke wa kafafu mai suna, The Medicals, ta kasar Masar ta yi gasa a karon farko a birnin Alkahira ranar Asabar, inda take fata wata ran za ta fafata a gasar cin kofin kwallon mutanen da aka yanke wa kada ta duniya.
A young man from Kenya's Maasai ethnic group poses after coming out of the bush on Wednesday after a month-long circumcision ceremony, which serves as a rite of passage to adulthood. Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wani matashi dan kabilar Maasai ta kasar Kenya ya fito daga daji ranar Laraba bayan an yi bikin yin kaciya na zamansa saurayi...
Circumcised Maasai young men wearing a ritual costume covered with hunted birds, come out from the bush to receive blessing from ceremony masters near Kilgoris, Kenya Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A lokaci guda kuma, wasu matasan sanye da 'tufafin' gargajiya na tafiya inda suka nufi wurin da manyan baki suke zaune domin su sanya musu albarka.
Chadian model Brigitte Tanegue is pictured during the 8th African Model Exhibition Awards on December 15, 2017, in Abidjan. Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A nan kuma 'yar kasar Chadi ce mai sanya kayan kawa mai suna Brigitte Tanegue ta yi kwalliya irin ta fure a wurin bikin nunin kaya ranar Juma'a da aka yi a Abidjan, babban birnin Ivory Coast ranar Juma'a
Georgian actors perform during "The Three Sisters" by Konstantin Purtseladze at the 19th session of Carthage Theater Days in Municipal Theater in Tunis, Tunisia, 15 December 2017. Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption A wannan ranar ce kuma dai wasu taurarin fim na Georgia suka yi wani wasa a Tunis, babban birnin Tunisiya.
A ranar Talata wasu 'yan mata suka yi wasan kwallon shinge a wani sansanin 'yan gudun hijira a yankin da 'yan Somaliya ke zama a Habasha. Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A ranar Talata wasu 'yan mata suka yi wasan kwallon shinge a wani sansanin 'yan gudun hijira a yankin da 'yan Somaliya ke zama a Habasha.
Daliban makarantar sojoji na Libya suna atisaye a ranar da ake yaye su daga makarantar sojojin ranar Litinin a makarantar da ke birnin Benghazi na gabashin kasar. Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Daliban makarantar sojoji na Libya suna atisaye a ranar da ake yaye su daga makarantar sojojin ranar Litinin a makarantar da ke birnin Benghazi na gabashin kasar.
A farm worker at a tobacco field at Herne Farm, 66 km south of Harare, Zimbabwe, 18 December 2017. The tobacco selling season is to start in March 2018. Zimbabwe is the biggest grower of tobacco in in Africa and sixth in the world. Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption A wannan rana kuma a Zimbabwe, wani ma'aikaci yana shanya ganyen taba don ya bushe bayan ya tsinko.
South African President and former President of the ANC Jacob Zuma departs following the closing ceremony on the final day of the 54th ANC conference at the NASREC Expo Centre in Johannesburg. Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A ranar Laraba, Shugaban Kasar Afirka Ta Kudu yana waka a wani taron jam'iyyarsa ta ANC bayan ya sauka daga shugabancinta.
Christmas decorations light up the streets of Lagos on December 18, 2017. Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Tun a ranar Litinin kuwa aka fara kawata birnin Lagos na NAjeriya da kwalliyar bikin kirsimeti.

Hotuna daga AFP da EPA da kuma Reuters

Labarai masu alaka