Kun san kasar Afirka da ta goyi bayan Trump kan Kudus?

Majalisar Dinkin Duniya ta yi watsi da kudurin shugaba Donald Trump da ya amince da birnin Qudus a matsayin babban birnin Isra'ila
Image caption Majalisar Dinkin Duniya ta yi watsi da kudurin shugaba Donald Trump da ya amince da birnin Qudus a matsayin babban birnin Isra'ila

Gwamnatin Amurka ta jinjina wa kasashen da suka goyi bayanta da wadanda suka kaurace wa kuri'ar da aka kada kan makomar birnin kudus a babban taron Majalisar Dinkin Duniya.

Babban zauren na Majalisar Dinkin Duniya ya yi watsi da babbar murya kan kudurin shugaba Donald Trump da ya amince da birnin Qudus a matsayin babban birnin Isra'ila.

Jekadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Nikki Hailey ta aike da sakon godiya ga jerin kasashe 66 da ta wallafa sunayensu a shafin twitter, tare da cewa hakan ba gazawa ba ce ga Amurka.

Tun da farko Nikki Hailey ta ce za su sa ido ga kasashen da suka juya wa Trump baya domin datse tallafin da suke samu daga Amurka.

Kasashen da suka goyi bayan Amurka.

Togo ce kasa tilo daga nahiyar Afirka da ta jefa kuri'ar adawa da kudirin Majalisar Dinkin Duniya da ya bukaci Trump ya janye amincewar da ya yi wa Qudus matsayin babban birnin Isra'ila.

Sannan kasashen da suka kauracewa kuri'ar sun kunshi Benin da Rwanda da Uganda da Sudan ta Kudu da kuma Malawi.

Tun kafin jefa kuri'ar, Shugaba Trump ya yi gargadin datse tallafin Amurka ga kasashen da suka ki mara ma shi baya a zauren na Majalisar Dinkin Duniya.

Akalla kasashen Afirka 37 ne suka goyi bayan kudirin Majalisar Dinkin Duniya da suka kunshi Najeriya da Ghana da Afirka ta Kudu da Masar da Habasha.

Sauran sun hada da Angola da Burkina Faso da Burundi da Congo da Ivory Coast da Botswana da kuma Eritrea.

Sai dai kuma wasu kasashen na Afirka da suka amince da kuri'ar sun fuskanci suka daga Isra'ila.

Ofishin jekadancin Isra'ila a Ghana ya fitar da sanarwar nuna rashin jin dadin yadda kasar ta goyi bayan kudirin Majalisar Dinkin Duniya.

Kiristoci na adawa a Ghana.

Kiristoci a Ghana sun bayyana adawa da matakin gwamnatin kasar na kin amincewa da Kudus a matsayin babban birnin Isra'ila.

Wasu manyan malaman kiristocin kasar sun danganta matakin a matsayin kuskure, musamman fargaba a kan barazanar Trump na datse tallafin da kasar ke samu daga Amurka.

Yawancin kasashen na Afirka dai na samun tallafin da ya shafi tsaro da tattalin arziki da raya al'umma daga Amurka.

Kuma sun juya wa Amurka baya ne duk da barazanar Trump na datse tallafin da suke samu daga kasar.

Botswana, ta fitar da wata sanarwa kafin jefa kuri'ar, tana mai cewa Amurka ba za ta tsoratar da ita ba.

Kasashe 128 ne suka amince da kudurin Majalisar Dinkin Duniya, yayin da kasashe tara suka jefa kuri'ar goyon Amurka kan amincewa da Kudus a matsayin babban birnin Isra'ila.

Kasashe 35 suka kauracewa zauren Majalisar.

Yanzu ba a san makomar birnin Kudus ba. Ko Amurka za ta sauya ra'ayinta?

Sannan wane mataki shugaba Trump zai dauka kan kasashen da suka jefa kuri'ar watsi da Kudus a matsayin babban birnin Isra'ila a Majalisar Dinkin Duniya?

Labarai masu alaka