Sweansea za ta nada sabon kociya

A watan Satumba ne Palace ta kori De Boer

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

A watan Satumba ne Palace ta kori De Boer

Swansea City na duba yiyuwar daukar tsohon kociyan Crystal Palace Frank de Boer da kuma tsohon kociyan West Ham United Slaven Bilic a matsayin wadanda zasu gaji Paul Clement.

A ranar Laraba ne Clement ya bar kungiyar da take ta karshe a teburin Firimiya.

A watan Satumba ne Palace ta kori dan kasar Netherland din De Boer bayan da ya jagoranci kungiyar wasanni biyar, yayin da shi kuma Bilic West Ham ta koreshi a watan Nuwamba.

Mai tsaron tsakiyar kungiyar kuma mai horarwa Leon Britton ne zai jagoranci kungiyar na wucin gadi a wasan da zasu karbi bakuncin Crystal Palace ranar Asabar.