Phil Foden ya tafi hutun jinya

Foden ya fafata a wasan da Ingila ta lashe gasar kofin duniya na 'yan kasa da shekara 17 a watan Oktoba.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Foden ya fafata a wasan da Ingila ta lashe gasar kofin duniya na 'yan kasa da shekara 17 a watan Oktoba.

Dan wasan tsakiyar Manchester City Phil Foden zai yi jinyar kusan wata hudu sakamakon raunin da ya yi.

Foden mai shekara 17, ya taka leda a minti na 89 na fafatwar da kungiyarsa ta yi nasara a kan Leicester a gumurzun da suka yi ranar Talata, kuma taka ledarshi na hudu a kungiyar a bana.

Foden ya fafata a wasan da Ingila ta lashe gasar kofin duniya na 'yan kasa da shekara 17 a watan Oktoba.

Kocin kungiyar Pep Guardiola ya ce abin takaici ne rashin dan wasan na tsawon wannan lokacin

A ranar Asabar ne City za ta kara da Bournemouth a filin wasa na Etihad, ranar 27 ga watan Disamba kuma za ta karbi bakuncin Newcastle.

City ita ce ta farko a teburin Firimiya da maki 51.