Trump ya yabi MDD kan takunkumin Koriya ta Arewa

Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong-un da shugaba Trump sun jima suna cacar baki Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong-un da shugaba Trump sun jima suna cacar baki

Shugaban Amurka Donald Trump ya jinjina wa kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya a kan kakabawa Koriya ta Arewa takunkumi mai tsauri.

A wani sako da ya rubuta a shafinsa na twitter, Mr Trump ya ce hakan ya jaddada cewa duniya na bukatar zaman lafiya ne ba kashe-kashe ba.

A cewar Amurka, Koriya ta Arewa ta shigar da gangar tattacen man fetur miliyan 4 da rabi a shekarar 2016.

Sai dai a yanzu wannan kudiri da a ka dauka zai kayyade ma Koriya ta Arewa ikon shigo da man fetur din zuwa ganga dubu 500 a shekara guda.

Hakan zai zaftare kusan kashi 90 a kudirin Kim Jong-un na son zama Shugaban kasar na har abada.

Fitar da man fetur din Pyongyang zai ragu da kusa kashi 90 cikin dari kuma za a bukaci 'yan Koriya ta arewar da ke aiki a wasu kasashen duniya da su dawo gida.

Kuma hakan zai dakile wata muhimmiyar kafa ta samun kudaden kasashen waje.

Labarai masu alaka