Guguwa ta hallaka sama da mutum 100

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Irin barnar da ta biyo bayan guguwar Tembin

Fiye da mutum 100 ne aka ba da rahoton guguwa ta hallakasu a yankin kudancin kasar Phippines, kuma ba a san inda gomman mutane suke ba.

Guguwar da aka saka wa sunan Tembin ta janyo ambaliyar ruwa da zaftarewar kasa a wasu sassa na tsibirin Mindanao.

Garuruwa biyu da abin ya fi shafa sune Tubod da Piagapo, inda zaftarewar kasa ta danne wasu gidaje.

Kasar Philippines na fuskantar guguwa mai karfin gaske akai-akai, amma abin lura shi ne bai cika shafan tsibirin Mindanao ba.

Guguwar Tembin, wacce aka fi saninta da sunan Vinta a Philippines ta fara karfi ne a Mindanao ranar Juma'a kuma hukumomi sun ayyana yanayin-ta-baci a wasu yankunana kasar.

Image caption Taswirar yankin da guguwar Tembin tafi shafa zuwa karfe 1 na ranar Asabar

Jami'ai masu aikin gaggawa sun ce an sami mace-mace akalla 62 a Lanao del Norte, 46 kuma a Zamboanga del Norte, inda aka sami akalla 18 a Lanao del Sur.

Shi ma wani jami'in dan sanda a garin Tubod, Gerry Parami ya fada wa AFP cewa akalla mutum 19 ne suka mutu a garin dake yankin Lanao del Norte.

Ya ce "Ruwan kogi ne yayi ambaliya har ya tafi da yawancin gidajen. Babu kauyen gaba dayansa."

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Masu aikin ceto na taimakawa mazauna Davao a tsibirin Mandanao

Matsalar rashin wutar lantarki da ta sadarwa tana dakile kokarin ceto mutane a yankin.

A makon jiya gomman mutane. suka rasa rayukansu a yayin da guguwar Kai-Tak ta auka wa yankin tsakiyar Philippines.

Wannan yankin bai gama farfadowa daga wata mahaukaciyar guguwa mai suna Haiyan ba, wacce ta kashe mutum fiye da 5,000, ta kuma tarwatsa miliyoyin jama'a daga muhallansu a 2013.

Labarai masu alaka

Karin bayani