Kun san yadda wani ya kirkiri injin bayar da wutar lantarki?

John Mwafute next to a row of dials in his power station
Image caption Mutanen kauyensu na kiransa da suna "mai cike da buri"

Wani dan kasar Tanzaniya John Mwafute ya kirkiro wani injin bayar da wutar lantarki a kauyensu.

John ya kirkiro injin din ne a kauyensu da ke kudancin Tanzaniya, inda ya ke ba wa gidaje sama da 250 wutar lantarki.

Kuma yana amfani ne da ruwan da yake kwararowa daga saman wani dutse da ke kusa da kauyen.

John ya yi aikin goge-goge bayan da ya daina zuwa makaranta. Amma kuma ba a son ransa yake aikin ba.

Sai dai yanzu injin samar da wutar da ya kirkiro na samar da wutar lantarki mai karfin 28kilowatts a kowacce rana.

Mutanen kauyensu na kiransa da suna "mai cike da buri".

Labarai masu alaka