Mota ta fada kogi da fasinjoji 50

Hukumomi sun ce yawancin wadanda abun ya rutsa da su mata ne da kuma kanannan yara.
Image caption Hukumomi sun ce yawancin wadanda abun ya rutsa da su mata ne da kuma kanannan yara.

'Yan sanda sun ce wata motar bas mai dauke da mutum 50 ta rikito daga kan gada a arewacin Indiya, a kalla mutum 32 suka mutu.

Rahotannin sun ce wani dan shekara 16 ne yake tuka motar inda bayan da ta kwace masa ta afka cikin ruwa sa'annan ta gangara cikin kogin Banas.

Rahotanni daga kasar sun ce motar na dauke da fasinjoji daga Rajasthan zuwa Ramdevji Hindu temple, wani wurin bautar Hindu da ke gundumar Sawai Madhopur.

An samu yawancin gawarwakin mutanen an kuma garzaya da wadanda suka jikkata zuwa asibitoticin kasar.

Hukumomi sun ce yawancin wadanda abun ya rutsa da su mata ne da kuma kanannan yara.

Jaridar Hindustan Times ta rawaito 'yan sanda na cewa direban motar na cikin wadanda suka mutu.

Labarai masu alaka