Buhari ya yaudari 'yan Nigeria- PDP

Tun bayan shan kaye a zaben shekarar 2015, jam'iyyar PDP ke sukar mulkin APC
Image caption Tun bayan shan kaye a zaben shekarar 2015, jam'iyyar PDP ke sukar mulkin APC

Jam'iyyar adawa ta PDP ta ce karancin man fetur da ake fuskanta yanzu alama ce da ke nuna cewa gwamnatin APC ta yaudari 'yan Najeriya ne.

A wata sanarwa daga kakakinta Kola Ologbondiyan, PDP ta ce duk da alkawarin da APC ta yi cewa matsalar karancin man fetur za ta zama tarihi idan ta karbi mulki, halin kuncin da 'yan Nigeria suka shiga yanzu abu ne da ya nuna cewa an yaudare su.

Jam'iyyar ta ce tun da Shugaba Buhari ya nada kansa babban ministan mai, bai kamata ba ya rika zargin wasu da rashin wadata kasar da man fetur ba.

Sai dai jam'iyyar APC mai mulki ta zargi Jam'iyyar adawa ta PDP da amfani da karancin man fetur da ake fuskanta don bata mata suna a idon 'yan kasar.

A wata sanarwa da kakakin Jami'iyyar Mallam Bolaji Abdullahi ya sanya wa hannu, APC ta ce tana sane da wahalhalun da 'yan Nigeria suka shiga sakamakon karancin man fetur musamman a lokacin bukukuwan kirsimeti.

Sanarwar ta kara da cewa gwamnati tana iyakacin kokarinta don kawo karshen matsalar nan ba da jimawa ba.

Labarai masu alaka