Dillalin wiwi ya afka motar 'yan sanda ya dauka tasi ce

File Picture dated 29/10/2003 of an unknown man smoking a cannabis joint / spliff / bifter. Hakkin mallakar hoto PA
Image caption 'Yan sanda sun ce mutumin na dauke da tabar wiwi kusan 1,000

Wani wanda ake tuhuma da dillancin tabar wiwi yayi wani abin takaici, bayan da fada cikin wata mota cikin hanzari dauke da daurin tabar ta wiwi 1,000 a tare da shi, kafin ya fahimci cewa motar ta 'yan sanda ce.

Jami'an 'yan sanda a Denmark sun ce mutumin na sauri ne ya isa gidansa a lokacin da yayi wannan batar basirar.

Wannan lamarin ya auku ne a Christiana, wani yankin babbban birnim kasar da akak kafa shi a shekarun 1970, kuma sanannen cibiyar cinikin haramtattun kwayoyi ne a kasar.

'Yan sandan sun ce zasu gurfanar da shi a gaban alkali, inda zai iya fuskantar dauri a gidan yari idan aka same shi da laifin cinikin tabar wiwi.

Ga yadda rahoton na 'yan sandan ya bayyan lamarin: "A jiya, wani dilan tabar wiwi daga Christiana wanda ke cikin saurin domin komawa gidansa ya fada bayan wata motar tasi. Amma ya sha mamaki bayan da ya fahimci cewa motar 'yan sanda ce ya shiga."

"Jami'an 'yan sanda dake cikin motar sun yi murna da ganinsa, tun da yan dauke da daurin tabar ta wiwi kimanin guda 1,000."

Dauka da dillancin tabar wiwi laifi ne a kasar ta Denmark.

Jami'an 'yan sanda sun yi ta kai samame cikin unguwar Christiana a watannin da suka gabata, domin neman zakulo dillalan haramtattun kwayoyi da tabar wiwi.

Karin bayani