Guatemala za ta mayar da ofishin jakadancinta birnin Kudus.

Shugaba Trump na Amurka ne ya fara sanar da yunkurin sa na mayar da ofishin jakadancin Amurkar zuwa birnin Kudus din daga Tel Aviv Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Shugaba Trump na Amurka ne ya fara sanar da yunkurin sa na mayar da ofishin jakadancin Amurkar zuwa birnin Kudus din daga Tel Aviv

Shugaban kasar Guatemala Jimmy Morales ya ce yana shirin mayar da ofishin jakadancin kasar da ke Israila daga birnin Tel Aviv zuwa birnin Kudus.

Kasar Guatemala na cikin kasashe bakwai da suka kada kuri'ar goyon bayan Amurka da Israila kan kudirin da MDD ta zartar.

Kudirin ya nemi Amurka ta sauya matsayin da ta dauka na ayyana birnin a matsayin babban birnin Israila.

Wakilin BBC ya ce gwamnatin shugaba Trump ta yi barazanar katse agajin da ta ke ba kasashen da suka bijire wajen kin goyon bayan ta.

Wasu na ganin mai yiwuwa wannan shi ne babban dalilin kasar na yin hakan.

Sai da shugaba Morales ya ce dama can Guatemala ta dade tana kawance da Israila.

Labarai masu alaka