Labaran da suka fi burge masu daukar hoto a Afirka a 2017

Men celebrate in Harare

Asalin hoton, Reuters

Ya ya za ku ji idan ku ka dauki hotunan wasu lokuta da manyan labarai suka faru a Afirka a shekarar 2017?

Wasu masu daukar hoto hudu sun gayawa BBC wani abu kan hotunan da suka fi so wadanda suka dauka a wannan shekarar.

Fitar farin dango (Hoton da ke sama)

Mike Hutchings shi ne babban mai daukar hoto na kamfanin dillancin labarai na Reuters a Kudancin Afirka. Mazaunin birnin Cape Town na Afirka Ta Kudu ne, ya yi bulaguro zuwa Zimbabwe a watan Nuwamba don yin labari a kan kwace mulkin da sojoji suka yi daga hannun Shugaba Robert Mugabe.

Tun safiyar ranar Mista Hutchings ya yi ta daukar hotuna a wajen majalisar dokokin kasar yayin da 'yan majalisar ke tattauna batun tsige Shugaba Mugabe.

Bayan ya gama daukar hotunan, sai ya yanke shawarar yin dan tattaki a wajen ginin majalisar a karo na karshe.

Yana tsayawa don neman tasi ne sai wani abokin aikinsa ya yi masa waya ya shaida masa cewa Shugaba Mugabe ya yi murabus.

Nan da nan sai Hutchings ya ruga kan titin da kamararsa inda ya ji ihun mutane, wadanda suka yi fitar farin dango don nuna murnarsu, shi kuwa sai ya dauki hotonsu.

Ya bayyana cewa: "Ina son yadda mutanen suka nuna karfinsu a hoton. Na ji dadin kasancewa a wajen a wannan lokacin har na shaidi abun da ya faru."

Yin kwalliya don zuwa makaranta

Babbar mai daukar hoto ta kamfanin dillanci labarai na Reuters a arewa maso yammacin Afirka Zohra Bensemra, ta yi bulaguro zuwa wani sansanin 'yan gudun hijira na wucin-gadi a Dallow da ke Somaliya, inda ta hadu da Zeinab.

Kamar sauran takwarorinta 'yan mata a duniya, Zeinab kan yi kwalliyarta a tsanake duk safiya kafin ta tafi makaranta.

Sai dai duk da cewa ba kamar miliyoyin sa'anninta ba, ita Zeinab 'yar shekara 14 tuni an yi mata aure, amma tursasata aka yi.

Iyeyen Zeinab na daga cikin kusan 'yan Somaliya 900,000 da suka tsere daga gidajensu, ba saboda yaki ba, sai dai saboda fari da hadarin fadawa cikin kuncin yunwa.

Sai dai tserewa zuwa sansanin na bukatar dumbin kudi, shi ya sa iyayenta suka bayar da aurenta kan sadakin dala 1,000, wanda zai ishe su su yi bulaguron.

Asalin hoton, Reuters

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Sai dai Zeinab ta ki yarda. Ta gudu ta buya a cikin daji, amma a karshe aka dawo da ita gida, aka kulle ta a daki aka kuma tilasta mata auren mutumin da ya girmeta da kusan shekara 40.

Iyayenta da ita kanta da kuma sabon mijin nata sun samu isa sansanin na Dallow.

Sai dai bayan kwana uku kacal da yin auren, Zeinab ba ta bata lokaci ba ta nemi saki, shi kuwa ya bukaci a biya shi kudinsa.

' Tafiya tamkar tauraruwa'

Bensemra ta fara ganin Zeinab ne a matsuguninta a wata safiya, inda hasken rana zai ba da damar daukar hoton yadda wannan matashiya ke gudanar da rayuwarta.

Wata kungiyar agaji ta Italiya ce ta ceto ta bayan kungiyar ta yi alkawarin biyan kudin.

A yanzu tana da 'yanci kamar sauran 'yan mata takwarorinta, har ma mai daukar hoton ta samu damar daukarta a yayin da take kwalliya don shirin tafiya makaranta.

Bensemra ta tambaye ta: "Me ya sa ki ke kwalliya idan za ki je makaranta?"

Sai Zeinab ta amsa da cewa: "Ina so na kasance kyakkyawa a ko yaushe."

Amma ba wannan ne ya fi jan hankalin Bensemra dangane da Zeinab ba. A maimakon haka, ta fi sha'awarta kasancewar ta wata matashiya mai tafiya makaranta dauke da litattafanta, tana tafiya tamkar tauraruwa."

"Ba ta mallaki komai ba amma tana son yin karatu - Na yi farin cikin haduwa da ita."

Sabon tabo

Wani mai daukar hoto dan Najeriya Akintunde Akinleye ya je Maiduguri, a arewa maso gabashin kasar, ya hadu da mutanen da ke yakar 'yan kungiyar Boko Haram.

A matsayinsa na dan Najeriyar da ke zaune a kasar Canada, mutane na yawan tambayar Akinleye ko yaki ake a fadin Najeriya baki daya.

"Wani bangare na kasar ne kawai," in ji shi. Da yawan 'yan Najeriya ba su ma san me yake faruwa a can ba, amma ya shafi kowa da ke kasar. Gagarumar matsala ce."

Amma Akinleye ya kagara sosai don son nuna wani bangare daban na yakin - bangaren da ya dauka kuwa na wannan hoton ne na wani dan shekara 38 mai suna Dala Aisami Angwalla, daya daga cikin 'yan kato da gora 30,000.

Asalin hoton, Akintunde Akinleye

Angwalla ya ji rauni a wani kwanton bauna da aka kai musu, amma Akinleye ba ya so mu fi mayar da hankali a can.

A maimakon haka, ya saita kamararsa kan mutumin amma ba a matsayin wanda ya ji rauni ba, sai dai a matsayin kamar wanda yake yi wa al'ummar duniya wata tambaya.

Mai daukar hoton ya ce: "Mutane na tunanin cewa duk wanda ke rayuwa a arewa maso gabashin Najeriya, musamman ma matasa, to 'yan kungiyar Boko Haram ne."

Amma Angwalla ya ce babu wani muhimmanci a gare shi ya tsaya cewa hakan ba gaskiya ba ne: Abun da ya fi muhimmanci shi ne ya kare gidansa da al'ummarsa daga kungiyar Boko Haram.

Abu ne mai wahala. Angwalla ya ce mayakan Boko Haram na zaune a cikin al'ummar tare da 'yan kato da garo.

"Mutanen da ke yakarsu sun san su, sun san dukkan mutanen da ke jawo matsaloli," in ji Akinleye.

Dankwali

Mai daukar hoto na Afirka Ta Kudu John Wessels ya yi bulaguro zuwa yankin Kasai a Jamhuriyyar Dimokradiyyar Congo a watan Agusta tare da kungiyar agaji ta Oxfam.

"Akwai wani yanayi na yin shiru, da tunani a wannan hoton," a cewar Wessels, yana mai nuna hoton Anny Mafutani, mai shekara 30.

Matashiyar, wadda tana daya daga cikin dubbai da suke tsere daga kauyenta don gujewa yaki, tana zagaye da duk wasu tarkace da ta samu tserewa da su, a wani coci da ake ajiye mutanen da ke neman mafaka.

Asalin hoton, John Wessels/Oxfam

Labarinta na son tsira da rayuwa na nan tas a kwakwalwar Wessels: Tun tuni aka hada wadannan kayan waje daya, tun kafin mayakan sa kan su kai musu farmaki.

Hakan na nufin a yayin da suka ji amsa kuwwar harbin bindiga, Mafutani da 'ya'yanta biyar sun shirya don tserewa daji.

Sai dai mijinta bai yi sa'a ba - an kashe shi a lokacin da yake kokarin tsira. Ba ta iya tsayawa don taimakonsa ba.

Mafutani da yaranta biyar sun shafe wata biyar a cikin daji. Babu isasshen abinci a cikin shirgin da suka kwasa, don haka sai ta kai su wannan cocin.

Amma duk da haka a lokacin da za a dauke ta hoto kokari take ta ga ta yi kyau sosai a hoton. Wannan ne ya sa ta bar Wessels cikin matukar mamaki.

"Ta iya daukar mutum biyar ta rayu da su a cikin daji, amma duk da haka tana son ta dauki dankwali ta daura don kawai ta yi kyau a hoto," in ji Wesells.

Dukkan masu daukar hoto hudun an yi hira da su ne a wani shiri na BBC World Service Focus on Africa, suna magana a kan ayyukansu don bayyana kadan daga cikin hotunan da suka zamo manyan labaran Afirka a wannan shekarar ta 2017.