Kun san sirrin garayar zinari ta Afirka Ta Kudu?

Sophie Ribstein
Image caption Wannan kayan kidin ya taba kasancewa wani abu mai sheki kan muhimman dandamali a Afirka ta Kudu

A shekarar 1962 Igor Stravinsky, mai kirkirar wakar gargajiya ta Turai dan asalin Rasha, wanda yana kuma jagorantar wake-wake, ya ziyarci hukumar talabijin ta Afirka ta Kudu domin ya jagoranci wasu jerin wakoki da za a yi.

Lokacin da ake tsaka da mulkin wariyar launin fata, gwamnatin ta yi imanin cewar wakar gargajiya ta Turai ta fararen fata ne kawai.

Wakiliyar BBC, Sophie Ribstein, ta yi waiwaye domin ta yi nazari akan ko an yi amfani da wata babbar garaya ta zinari a taron wakokin.

Bincikenta tamkar komawa lokacin da can ne. An lullulbe bangwayen da darduma mai ruwan kasa.

Da na shiga zauren hedikwatar hukumar talabijin din Afirka ta Kudu, SABC, tamkar ina tafiya ne a shekarun 1970s, a lokacin da gwamnatin wariyar launin fata take iko da ginin tare da mamaye rediyo da talabijin din kasar.

SABC ta taba kasancewa muhimmiyar kafar watsa farfaganda ta gwamnatin wariyar launin fata.

Sannan na yi wata kwana, na tura wani get, sannan na shiga dakin adana wakoki... kuma komai ya sauya.

Na zo ne domin in ga wani abin tarihi na wancan lokacin - wata garayar zinari ta wancan lokacin, wadda fitaccen mai hada garaya na Amurka Lyon and Healy ya sassaka.

Wannan kayan kidin ya taba kasancewa kan mumman dandamali a kasar.

Image caption Sautin garayar tana nan yadda take a da

A wancan lokacin babban mai kada garaya na gidan kade-kade na hukumar SABC shi ne yake kada garayar tarukan wakar gargajiya ta Turai - wadda a wancan lokacin fararen fata ne kawai ake kyalewa su halarci taron.

A halin yanzu kasaitattciyar garayar, ta yi shiru, karkashin wani lullubin kare datti a gefen wani daki na lokacin da.

Ni ma kaina ina kada garaya, kuma na ji labarin wannan kayan kidan daga mutumin da ya hada mini garayata a Faransa.

Na cire lullubin garayar a hankali, kuma na zauna sannan na rungumeta da kafadata ta dama.

Zuciyata ta kara sauri. Da na fara kadata, yatsuna suka motsa daga waya zuwa waya, sautin da ya fito tatacce ne kuma mai cike da ma'ana, na ji dadi tare da gamsuwa.

Har yanzu sautinta na nan kamar yadda yake a da can.

Image caption garayar mai matukar tsawo tana nan cikin nagarta

A lokacin da mulkin wariyar launin fata ya zo karshe a shekarun 1990, an rufe gidan wakar farare na SABC, kuma an adana abubuwan gidan wakar a cikin dakin adana abubuwa.

Tare da kayayyakin waka akwai daruruwan da kuma dubban rubutattun wakoki, wadanda yawancinsu aka rubuta su da hannu cikin wasu abubuwan tarihi na wannan lokacin.

A kan bangon, na ga wasu hotuna marasa kala .... na Igor Stravinsky a Afirka ta Kudu.

Na yi tunanin me ya sa wannan fitaccen mai kirkirar waka dan asalin Rasha ya zo nan?

A shekarar 1962 ne ya ziyarci kasar wadda take cikin tashin hankali a wancan lokacin saboda gwamnatin wariyar launin fata da ke danne hakkin tofa albarkacin baki.

Hakkin mallakar hoto .
Image caption An gayyaci Stravinsky domin ya yi wasa wa farare kadai, amman ya hakikance akan cewa zai yi wasa a gaban bakake 'yan Afirka ta Kudu ma

Daga baya na gano cewa, an gayyaci Stravinsky domin ya gudanar da wakar gidan kade-kade na hukumar SABC, amma abin da ya fi jan hankali dangane da ziyararsa, shi ne ya dage cewa dole sai ya yi wasa gaban bakake.

Hukumomi sun ba shi damar yin hakan a KwaThema, wani garin bakake da ke da nisan kilomita 40 daga birnin Johannesburg.

"Ina son in yi waka a gaban 'yan Adam ne kawai ," in ji mawakin.

"Na so in san yadda bakaken da suka kalli wakar suka ji dadinta.

Ta yaya ma suka ji labarinsa a daidai lokacin da gwamantin take ganin irin wannan wakar ta fararen fata ne kawai?

Yarima Thethe zai iya tunawa da wakar da ya yi.

"Na hadu da mawakin mai tsayi kuma mai shakara 82 a cikin katafaren dakin taro mai suna KwaThema, inda Stravinsky ya yi waka.

Sai mutum ya ji yana ko ina.

"Wancan lokacin ne karon farko da na tsaya kusa da gidan kade-kade! Na kasa yarda da cewa da gaske hakan na faruwa!

A daidai lokacin da hannayen Stravinsky suka yi sama, wakar kuma ta kayatar da masu kallo matuka," kamar yadda ya shaida mini yana mai zakuwa kamar wanda zai hau kan dandamali domin ya kwaikwayi kwararren mawakin.

"Ana guda, ana fito! Amma da zarar an fara wakar, ko ina ya yi tsit ta yadda idan allura ta fadi za ka ji."

A lokacin mulkin wariyar launin fata, ya ce, shiga shagon sayar da faya-feyin waka ya kasance haramtaccen abu.

Na zayyana wurin da abin ya faru a kaina: dubban mutane sun hallara a wannan dakin taron, suna jin ko wnne sauti, suna kallon ko wanne motsi da mawakan suka yi da kuma dan Rasha gajere da ke jagorantar makadan.

A bayan dakin taron, shin jitar zinaren ta kasance a wurin ne?

A lokacin da wani abokin aikina na BBC ya yi kicibis da wakar makadan da aka nada a fai-fai a wurin adana kayan tarihi na hukumar gidan talabijin ta Afirka ta Kudu (SABC), mun saurarri wakoki daga The Fireworks Suite da kuma kadan daga cikin wakokin Pulcinella da Petrushka a hankali.

Hakkin mallakar hoto .
Image caption Wakar da Stravinsky ya yi a gaban bakake ta karya dokar mulkin wariyar launin fata

Ta yiwu ba a saurari faifayin wakar ba cikin shekara 55. Wannan ya sosa mana rai.

Amman babu alamar garayar cikin wakar da aka nada. Abu ne mai jan hankali, amman wani sirri ne da ba a gano bakin zarensa ba.

Kuma yayin da nake tunanin wannan tarihin, wata rana na zauna a bayan kayan kidana a gida kuma na saka wata gajeruwar waka wadda Igor Stravinsky ya yi a karshen ziyararsa.

Ya gina wakarsa ne bisa sautin "S, A, B, C" - S wanda ke daidai da E mai shimfida - domin ya gode wa gidan kade-kaden doa gayyatar da ta yi masa.

Labarai masu alaka