An gano gawar wani alkali da aka sace a Saudiyya

Alkalin, dan shi'a ne tsiraru a kasar Saudiyya da ke korafin cewa 'yan sunna masu rinjaye sun mayar da su saniyar ware. Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Alkalin, dan shi'a ne tsiraru da ke Awamiya a kasar Saudiyya da ke korafin cewa 'yan sunna masu rinjaye sun mayar da su saniyar ware.

'Yan sandan Saudiyya sun ce sun gano gawar wani alkalin da aka sace shekara daya da ta wuce.

An gano gawar Sheikh Mohammed al-Jirani ne bayan wani artabu a makon da ya wuce tare da wasu da ake zargin 'yan gwagwarmaya ne a wata gona a gabashin kasar.

Alkalin, dan shi'a ne tsiraru da ke birnin Awamiya a kasar Saudiyya da ke korafin cewa 'yan sunna masu rinjaye sun mayar da su saniyar ware.

Sheikh Jirani dai ya sha sukar zanga-zangar da 'yan shi'a ke yi, kuma ya zargi manyan malamai a cikin al'ummar shi'a din da kasancewa kut-da-kut da Iran.

A watan Disambar 2016 ne aka sace Sheikh Mohammed al-Jirani a gaban gidansa da ke birnin Awamiya.

A wancan lokacin hukumomi sun ce sun kama mutum uku da ake zargi da hannu a sace shin.

Kafofin yada labaran kasar sun ce dama an sha hakon alkalin a wasu hare-hare da aka sha kai wa kafin daga bisani a sace shi.

Labarai masu alaka