Nigeria: Sojoji sun dakile harin Boko Haram a Maiduguri

Rundunar sojin Najeriya dai ta sha yin ikirarin cin galaba kan mayakan kungiyar ta Boko Haram Hakkin mallakar hoto NIGERIAN ARMY
Image caption Rundunar sojin Najeriya dai ta sha yin ikirarin cin galaba kan mayakan kungiyar ta Boko Haram

Rundunar sojin Najeriya ta ce ta dakile wani hari da 'yan kungiyar BokoHaram su ka yi yunkurin kai wa a birnin Maiduguri a ranar Kirsimeti.

Kwamandan rundunar sojojin ta Lafiya Dole a yankin arewa maso gabashin kasar Major Janar Nicholas Rogers shi ne ya bayyana haka a wata sanarwa.

Ya ce dakarun sojin sun yi bata kashi da masu tayar da kayar bayan da suka farma wani wurin binciken ababen hawa na sojoji da ke wajen birnin a cikin motocin a kori kura.

Janar Nicholas Rogers ya ce an kwashe sama da awa guda ana artabu tsakanin mayakan da sojoji.

Sanarwar ta ce babu asarar rayuka sai dai a lokacin da maharan ke tserewa sun kona wasu motoci biyu da wasu gidaje da ke kusa.

Hukumomi a birnin Maiduguri sun ce an kara tsaurara matakan tsaro a lokacin bukukuwan Kirsimeti.

Labarai masu alaka