Ana zaben shugaban kasa zagaye na biyu a Liberia

Ofishin hukumar zabe ta Liberiya a birnin Monrovia

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Ofishin hukumar zabe ta Liberiya a birnin Monrovia

A ranar Talata ne ne ake zaben shugaban kasa a Laberiya zagaye na biyu.

'Yan takara biyu ne dai za su fafata a zaben wanda shi ne karon farko da kasar ke shirya zabe don mika mulki daga wata sabuwar gwamnati zuwa wata tun bayan yakin basasar kasar.

Mataimakin shugaban kasar mai ci Joseph Boakai da kuma shahararren tsohon dan wasan kwallon kafan nan George Weah sune ke fafata wa.

Wasu dai na ganin hukumar zaben Laberiya ta yi gaggawar sake shirya zaben zagaye na biyu kafin shekarar ta kare.

Sai dai a hira da BBC, tsohon shugaban Nigeria Goodluck Jonathan, ya ce hukumar zaben ba ta yi gaggawar shirye zaben ba.

Mr Jonathan wanda ke jagorantar tawagar masu sa ido daga cibiyar bunkasa dimokradiyya ta National Democratic Institute, ya ce Laberiya tana da kalubale da dama na yadda shugaban kasa mai ci za ta mika mulki ga zababben shugaba.

Ya kara da cewa hakan zai nuna wa duniya cewa mulkin dimokradiya ya kafu sosai a Laberiya, kuma abun da ya rage shi ne a bunkasa tattalin arzikin kasar.