Saudiyya ta hana 'yan Isra'ila iznin shiga kasarta yin gasar dara

Attendees play chess for fun as they attend at the King Salman Rapid Blitz Chess Championships opening in Riyadh, Saudi Arabia, December 25 Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption An fara gasar wasan dara ta duniya ta Rapid and Blitz Chess a Riyadh da ce-ce-ku-ce

An fara gasar wasan dara ta duniya a Saudiyya da ce-ce-ku-ce, bayan da kasar ta hana 'yan wasan Isra'ila izinin zuwa.

Wani jami'in Saudiyya ya ce ba za a iya bai wa 'yan Isra'ila izinin shiga kasar ba saboda babu wata alakar diflomasiyya tsakanin masarautar kasar da Isra'ila.

Hukumar Wasan Dara ta Isra'ila ta ce za ta nemi a biya ta diyyar kudi.

Ana ganin karbar bakuncin wannan gasa da Saudiyya ta yi a matsayin budewa kanta wata hanya ta yin mu'amala da sauran kasashen duniya sosai.

Amma 'yar wasan da ke rike da kambun gwarzuwa ta duniya ta ce ba za ta je gasar ba saboda ba ta son sanya abaya, wato riga mai tsawo da mata ke sawa kafin su fita bainar jama'a a Saudiyya.

Anna Muzychuk mai shekara 27 wadda ke yi wa kasar Ukraine wasa ta ce, "duk da irin makudan kudin da za a bai wa wanda ya yi nasara, ni ba zan je Riyadh wannan wasa ba," ko da hakan na nufin ta rasa kambunta biyu da take rike da su.

Gasar Dara ta kungiyar Sarki Salman ta Rapid and Blitz Chess, ta sanya kyautar dala 750,000 a wasan bude gasar, da kuma dala 250,000 a gasar mata.

Ta yi rubuta a shafinta na Facebook inda take ba da misali da wata gasa ta duniya da aka yi a Tehran babban birnin Iran a farkon shekarar 2017, kamar haka: "Na yi ta sa rayuwata a hadari ina sanya abaya ko yaushe? Komai yana da makura, dankwalin da na sanya a Iran ma ya ishe ni."

A wani rubutun kuma da ta yi a ranar 23 ga watan Disamna cewa ta yi duk da cewa za ta ji bacin ran rasa kambunta, hakan ba zai hana ta tsayawa a kan ka'idojinta ba.

Ms Muzychuk ta nuna wannan kin amincewar ne a lokacin da ake samun karuwar mayar da hankali kan 'takurar' da mata ke fuskanta kan 'yancinsu a Saudiyya.

A yayin da aka dage dokar haramtawa mata tukin mota daga tsakiyar shekara mai kamawa, masu fafutuka sun ce kasar na da sauran aiki a gabanta wajen inganta daidaton jinsi da hakkin dan adam.

Mai rike da kambun wasan dara na uku a duniya dan kasar Amurka Hikaru Nakamaru, ya ce yanke shawarar yin wannan gasa a Saudiyya 'abun tsoro ne.'

A yayin da 'yan wasa bakwai daga Isra'ila ba za su samu damar halartar wasan ba bayan hana su izinin shiga kasar da hukumomin Saudiyya suka yi, 'yan wasan Qatar da Iran za su samu damar zuwa bayan da aka ba su izinin shiga a kurarren lokaci, duk kuwa da irin lalacewar da dangantaka ta yi tsakanin kasashensu da masarautar Saudiyyar.

Hukumar Dara ta Isra'ila ta ce da fari ta yi amannar cewa za a bar 'yan wasanta su shiga, duk da cewa babu dangantakar diflomasiyya a tsakanin kasashen biyu.

Ta soki Saudiyya da yi wa Hukumar Dara ta Duniya rufa-rufa don ta samu damar karbar bakuncin gasar.

Labarai masu alaka

Karin bayani