An kafa dokar takaita zirga-zirga a Bwarin Abuja

Wutar da aka cinna wa kasuwar Bwarin dai ta kone dukkan shagunan da ke ciukin kasuwar
Image caption Wutar da aka cinna wa kasuwar Bwarin dai ta kone dukkan shagunan da ke cikin kasuwar

An kafa dokar takaita zirga-zirga a garin Bwari da ke babban birnin tarayyar Najeriya, Abuja, kwana daya bayan wani rikici mai nasaba da kabilanci ya haddasa salwantar rayuka da kadarori.

An kafa dokar takaita zirga-zirgar ne daga karfe shida zuwa shida yayin da aka tabbatar da mutuwar mutum uku a hukumance sakamakon rikicin.

Duk da cewa hukumomi ba su fayyace iya abin da aka rasa a kasuwar garin da aka cinna wa wuta ba, abokin aikinmu Abdulwasiu Hassan da ya ziyarci garin na Bwari, ya ce an kone kasuwar garin da kuma wasu shaguna ciki har da shagunan da ke gefen reshen bankin Zenith na garin.

A lokacin da wakilinmu ya ziyarci kasuwar garin, ya tarar da masu shaguna suna neman dan abin da za su iya samu daga cikin shagunansu wadanda galibinsu sun kone kurmus.

Mallam Ibrahim Saidu ya shada wa BBC cewa, yana kokarin tsamo buhunhunan shinkafar da ba su gama konewa daga shagon dan uwansa ne.

Hakkin mallakar hoto Abdulwasiu Hassan
Image caption Masu shaguna da sauran mutane sun fito domin ganin abin da ya faru a garin Bwari da safiyar Talata

Mallam Ibrahim ya ce dan uwansa mai shagon ya rasa shagunan sayar da kayan abinci da wuta ta kone a kasuwar.

Daya daga cikin 'yan kasuwar da shagonsa ya kone, Godwin Onah, ya ce ya rasa naira miliyan biyar a shagonsa.

Godwin ya ce: "Ina cikin gida ina shan bukin Kirstimeti, sai wani ya kira ni a waya ya ce kasuwar Bwari na ci da wuta.

"Da muka isa wajen wancan gidan man, sai aka ce an toshe hanya. An hana mutane isa ga kasuwar.

"Da safiyar yau Talata da na zo na ga komai ya kone. Ban samu komai ba. Ban tsira da ko allura ba daga shagona, ko allura daga cikin kayayyakin nake sayarwa.

"Kayayyakin da na rasa a cikin shagon tare da cinikin da na yi na lokacin Kirsimeti ya kai naira miliyan biyar," in ji Onah.

A lokacin da ake hada wannan rahoton dai sojoji da 'yan sanda na ci gaba da sintiri a garin na Bwari.

Image caption Masu shaguna da dama sun yi ta kokarin neman abin da za su iya samu daga tarkacen shagunansu

Labarai masu alaka