Tsohon minista zai sha daurin shekara 22 a Ivory Coast

Hubert Oulaye Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Hubert Oulaye tsohon na hannun daman Laurent Gbagbo ne

An yanke wa tsohon ministan Ivory Coast Hubert Oulaye hukuncin shekara 22 a gidan Kaso, bayan samunsa da hannu a kisan mutane 18 ciki har da dakarun wanzar da zaman lafiya 7 na Majalisar Dinkin Duniya a shekarar 2012.

Babban lauyan gwamnatin kasar ya ce Mista Oulaye wanda shi ne ministan yada labarai na lokacin mulkin Shugaba Laurent Gbagbo, ya samar da wata kungiyar 'yan tawaye tare da ba ta kudade a yammacin kasar.

Sai dai tsohon ministan ya musanta tuhumar da cewa an yi ta ne kawai domin kawai a bata masa suna, sannan lauyansa ya ce za su daukaka kara a kan hukuncin.

Harin na shekarar 2012 ya faru ne a daidai lokacin da Ivory Coast ke kokarin farfadowa daga tashin hankalin da aka yi bayan zaben Shugaba Gbagbo ya ki amincewa da shan kaye bayan sanar da Alassane Ouattara a matsayin sabon shugaban kasa.