'Mutum miliyan 30 na fuskantar barazana a Tafkin Chadi'
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

'Mutum miliyan 30 na fuskantar barazana a yankin Tafkin Chadi'

Hukumomi na kasashen yankin Tafkin Chadi na ci gaba da nuna damuwa kan yadda tafkin ke ci gaba da kankancewa cikin shekarun baya-bayan nan inda suka ce adadin ruwan ya ragu da kamar kashi 90 cikin 100 duk da muhimmancin da ya ke da shi ga miliyoyin mutane.

Don haka ne kasashen yankin su shida tare da hadin gwiwar Majalisar Dinkin Duniya ke shirin gudanar da wani taro a Nijeriya, irinsa na farko a tarihi, cikin watan Faburairu da ke tafe da nufin nemo hanyoyin hana tafkin bacewa baki daya.

Ishaq Khalid ya tuntubi Alhaji Sanusi Imrana Abdullahi, shi ne Sakataren Gudanarwa na Hukumar Kula da Yankin Tafkin Chadi domin jin karin bayani kan halin da tafkin ke ciki.

Latsa alamar lasifikar da ke sama domin jin hira da Alhaji Sanusi Imrana Abdullahi.

Labarai masu alaka