Kalli hotunan abubuwan da suka faru a duniya a 2017

Hotunan wasu labaran da suka fi jan hankali da muka zabo dominku daga sassa daban-daban na duniya a shekarar da ke karewa ta 2017.

An Eritrean Orthodox Christian pilgrim is baptised at the Qasr El-Yahud baptism site on the west bank of the River Jordan. Hakkin mallakar hoto ABIR SULTAN/ EPA
Image caption A nan ana yi wa wata mai bin addinin kirista daga Eritriya a Qasr El-Yahud da ke bangaren Yamma da Kogin Jordan, wankan tsarki na baftisima. Wannan ne wurin da kirista suka yi imanin cewa Annabi Yahaya ya yi wa Isa Al-Masihu baftisima. Sabili da yanayin rikice-rikicen addini a wurin ne aka kulla wata yarjejeniya tsakanin gwamnatin Isra'ila da hukumar Falasdinawa tare da wasu dariku bakwai domin masu ziyara su sami damar zuwa wurin.
Kandy Freeman participates in a Black Lives Matter protest in front of Trump Tower in New York City, on 14 January 2017. Hakkin mallakar hoto Stephanie Keith/REUTERS
Image caption Ita kuma Kandy Freeman ta shiga wata zanga-zanga ta "Black Lives Matter" a gaban ginin Trump Tower da ke birnin New York. An shirya wannan zanga-zangar ne a Amurka domin mayar da martani saboda kisan bakaken fata da 'yan sanda ke yi a Amurka.
A moth lands on the nose of Rafael Nadal. Hakkin mallakar hoto LUKAS COCH/ EPA
Image caption Wani kwaro ya sauka a kan hancin Rafael Nadal na Spaniya a yayin da yake fafatawa da Milos Raonic na kasar Canada a gasar wasan tennis da aka yi a Australia.
President Donald Trump takes the oath of office from Supreme Court Chief Justice John Roberts on the West Front of the U.S. Capitol on 20 January 2017 in Washington, DC. In today's inauguration ceremony Donald J Trump becomes the 45th president of the United States. Hakkin mallakar hoto Alex Wong/Getty Images
Image caption Ranar 20 ga watan Janairu ne aka rantsar da Donald J Trump a matsayin shugaban Amurka na 45 a birnin Washington, yayin da matarsa Malania ke kallon bikin. A jawabinsa bayan an rantsar da shi, ya sha alwashin tsaya wa Amurkawan da aka "manta da su", kuma ya ce "kasarmu za ta sake samun daukaka".
Khalil Hymore Quasha and his daughter Norah Quasha participate in the Women's March on Washington. Hakkin mallakar hoto Lucy Nicholson/ Reuters
Image caption An gudanar da fiye da maci 600 a sassan duniya daban-daban a ranar farko ta mulkin shugaba Trump na Amurka. A birnin Washington DC, Khalil Quasha ya dauki 'yarsa mai shekara shida a bisa kafadunsa.
A golden eagle grabs a flying drone. Hakkin mallakar hoto Regis Duvignau/ Reuters
Image caption A yankin kudu maso yammacin Faransa, wani maiki mai ruwan zinari ya kama wani karamin jirgi mai sarrafa kansa a yayin da ake wani atisayen soji a sansanin Mont-de-Marsan na sojin sama.
Children dressed as Charlie Chaplin pose for a group photo. Hakkin mallakar hoto LAURENT GILLIERON/ EPA
Image caption Fiye da mutum 600 sun halarci wani bikin tunawa da shahararren mai wasan barkwancin nan, Charlie Chaplin, inda suka yi shiga irin tasa a Corsier-sur-Vevey. Chaplin ya mutu ne a wannan garin bayan da ya shafe shekara 24 a cikinsa.
Italy's Mount Etna, Europe's tallest and most active volcano, spewed lava as it erupted on the southern island of Sicily, Italy on 28 February 2017. Hakkin mallakar hoto Antonio Parrinello/REUTERS
Image caption Dutse mai aman wuta na Mount Etna da ke Italiya ya amayar da narkakken dutse da wuta a tsibirin Sicily da ke kudancin kasar a watan Fabrairu.
Aibhin Kenneally aged 13 from the Flynn-O'Kane dance group warms up backstage. Hakkin mallakar hoto Clodagh Kilcoyne/ Reuters
Image caption Yarinya 'yar shekara 13 da haihuwa, Aibhin Kenneally na motsa jiki gabanin gasar rawar 'yan Irish ta duniya da aka yi a birnin Dublin.
The sun reappears behind the moon during a full eclipse in Sisters Oregon, USA. Hakkin mallakar hoto MONICA M. DAVEY/ EPA
Image caption Ranar 21 ga watan Agusta, fiye da mutum miliyan bakwai a fadin Amurka suka kalli kusufin ranar da ya ratsa kasar daga tekun gabas zuwa tekun yamma, a karon farko tun 1918. A garin Sisters na jihar Oregon, ranar ta leko kadan bayan wata. An dai gargadi jama'a game da hatsarin kallon kusufin da idanunsu kai tsaye.
Photographers help a Rohingya Muslim to come out of Naf River. Hakkin mallakar hoto Hannah McKay/ Reuters
Image caption A wannan hoton ana iya ganin masu daukar hoto na taimaka wa wata Musulma 'yar Rohingya don ta sami ficewa daga kogin Naf a hanyarta ta zuwa Bangladash daga Myanmar. 'Yan Rohingya Musulmai ne da ba su da kasa tasu ta kansu da aka dade ana muzguna musu a Myanmar. Fiye da mutum 647,000 sun tsere zuwa kasar Bangladesh tun da rikici ya barke a watan Agusta.
Caleb Amisi Luyai, an opposition politician, reacts after a gas canister fired by policemen hits his car. Hakkin mallakar hoto Baz Ratner/ Reuters
Image caption Rikici ya barke a birnin Nairobi na kasar Kenya a yayin da ake kada kuri'a a zagaye na biyu na zaben shugaban kasa da aka yi. Ana iya ganin wani dan majalisa kuma dan adawa, Caleb Amisi Luyai, yana kokarin fito da kansa waje bayan da hayaki mai sa hawaye ya turnuke motarsa bayan da 'yan sanda suka yi kokarin dakile macin da 'yan adawar ke yi a babban birnin kasar.
North Korean leader Kim Jong Un watches the launch of a Hwasong-12 missile. Hakkin mallakar hoto KCNA/ Reuters
Image caption A watan Satumba, shugaban Koriya Ta Arewa Kim Jong-un ya kalli yadda kasarsa ta harba makamin rokar Hwasong-12. Kasar ta yi gwaje-gwajen rokoki masu linzami a yayin da kasashen duniya ke nuna damuwarsu.
Fire fighters rest during a wildfire at Penela, Coimbra. Hakkin mallakar hoto PATRICIA DE MELO MOREIRA/AFP
Image caption Masu kashe gobara na hutawa a lokacin da suke kokarin kashe gobarar daji a Panela na yankin tsakiyar Portugal. An sami irin wannan gobarar dajin a yankunan arewaci da tsakiyar kasar da suka zama sanadin mutuwar fiye da mutum 30 kuma gomman mutane suka sami raunuka bayan wani yanayi na zafin da rashin ruwan sama da ya shafi yankunan.
Spanish Civil Guard officers remove demonstrators outside a polling station for the banned independence referendum. Hakkin mallakar hoto Susana Vera/ Reuters
Image caption 'Yan sandan Spaniya na kokarin kawar da masu zanga-zanga a wata cibiyar zabe da ke birnin Barcelona a ranar da aka gudanar da zaben raba gardamar zaman yankin Kataloniya a kasar ta Spaniya. Daga baya gwamnatin Spaniya ta mayar da yankin karkashin mulkinta kai tsaye.
Ushers throw their hats in the air as they pose for photographers at the Tiananmen Square. Hakkin mallakar hoto Thomas Peter/ Reuters
Image caption A Beijing, babban taron kasa na jam'iyyar gurguzu ta kasar Sin ya duba batun wanda zai jagoranci kasar a wa'adin mulki da ke gaba. Shugaba mai ci Xi Jinping ya cigaba da jagorantar jam'iyyar na wa'adin shekara biyar masu zuwa, a babban taron jam'iyyar na gaba.
Bonskot Chaisuwan cries as she joins everyone in singing the Royal anthem. Hakkin mallakar hoto Paula Bronstein/ Getty Images
Image caption Bayan shekara guda, an kammala zaman makokin tsohon Sarkin Thailand Bhumibol Adulyadej wanda ya mutu a bara. Shi ne sarki wanda yafi dadewa a bisa karagar mulki a duniya, bayan da ya shafe shekara 70 yana mulki. Ya rasu yana da shekara 88 da haihuwa.
A migrant arrives at a naval base. Hakkin mallakar hoto Ahmed Jadallah/ Reuters
Image caption Wani dan ci-rani a tashar sojin ruwa a Triopli, bayan da sojin ruwa na Libya suka ceto shi daga tekun Bahar Rum. Dubban daruruwan 'yan ci-rani daga yankin Afirka Ta Yamma sun rika ratsa hamadar Sahara da Bahar Rum a kokarin isa Turai.
A young woman walks between tombstones. Hakkin mallakar hoto LIANNE MILTON/ PANOS
Image caption A kasar Guatemala, wata budurwa ke tafiya tsakanin kaburbura a yayin da ake gudanar da bikin ranar matattu a wata makabarta da ke garin. An rika yin wasanni da jiragen leda irin wadanda yara kan hada domin wai su kore muggan aljanu, ko matattun sa samu damar karbar kyaututtukan da suka kai musu.
Actor Rose McGowan raises her fist at a podium. Hakkin mallakar hoto Rebecca Cook/ Reuters
Image caption 'Yar fim Rose MvGowan ta dunkule hannunta kuma ta daga shi sama bayan ta gabatar da jawabi a wajen wani taro na mata a birnin Detroit, na jihar Michigan. Fitowarta ta farko kenan bayan da ta zargi babban furodusan fina-finai Harvey Weinstein da yi mata fyade. Ms McGowan na cikin mata masu yawa da suka zargi Mr Weinstein da yi musu fyade. Ya musanta dukkan zarge-zargen, inda ya ce ya kwanta da matan ne a bisa yardarsu da amincewarsu.
Shoppers reach out for television sets as they compete to purchase retail items on Black Friday. Hakkin mallakar hoto Paulo Whitaker/ Reuters
Image caption A wani shago da ke birnin Sao Paulo na kasar Brazil, mutane na rububin sayen talabijin a ranar da ake karyar da farashin kayayyaki, wacce aka fi sani da Black Friday. Wannan al'ada ta fara ne a Amurka inda a ko wacce shekara ake rage farashin kaya dab da lokacin bukukuwan kirsimeti.
Zimbabweans celebrate after President Robert Mugabe resigns in Harare, Zimbabwe, 21 November 2017. Hakkin mallakar hoto Mike Hutchings/REUTERS
Image caption 'Yan Zimbabwe na murnar saukar Shugaba Robert Mugabe, lamarin da ya kawo karshen mulkinsa na shekara 37. Emmerson Mnangagwa ya gaje shi bayan da aka shafe mako guda cur ana takardama game da saukarsa daga mulki, bayan kuma sojojin kasar sun kwace mulki.
A man holds a baby at the border wall between Mexico and United States, during the "Keep our dream alive" event, in Ciudad Juarez, Chihuahua state, Mexico on 10 December 2017. Hakkin mallakar hoto HERIKA MARTINEZ/AFP
Image caption Wani mutum ya rike 'yarsa a jikin shingen da ke iyakar Mexico da Amurka. A ranar 'Yanci ta Duniya, a kan kyale iyalan da iyakar ta raba su gana na minti uku a iyakar da ke Ciudad Juarez Park a Mexico da Sunland na jihar New Mexico a Amurka.

Dukkan hotunan suna da hakkin mallaka