Fitattun 'yan Nigeria da suka mutu a 2017

Ahmadu Chanchangi

Hakkin mallakar hoto Facebook
Image caption Ahmadu Chanchangi fitaccen dan kasuwa ne

Fitaccen dan kasuwa kuma Shugaban kamfanin jiragen sama na Chanchangi Airlines a Najeriya Alhaji Ahmadu Chanchangi Allah ya yi masa rasuwa ne a watan Afrilu, a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja, yayin da ake kokarin kai shi wani asibiti da ke Abuja.

Marigayin ya yi doguwar jinya gabanin rasuwarsa.

Rahotanni sun ce marigayin ya rasu ya bar mata biyu da 'ya'ya 33 cikinsu har da dan Majalisar Wakilai daga Jihar Kaduna Alhaji Rufa'i Chanchangi.

Danbaba Suntai

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Suntai fitaccen masanin ilimin hada magunguna ne

Tsohon gwamnan jihar Taraba Danbaba Danfulani Suntai ya rasu ne a watan Yuni yana da shekara 56, bayan ya shafe kusan shekara hudu yana jinyar hatsarin da yayi a cikin jirgin saman da yake tukawa.

Dan Fulani Suntai ya zama gwamnan jihar Taraba ne ranar 29 ga watan Mayun shekarar 2007, kuma ya sake komawa kujerar a shekarar 2011, amman jirgin da yake tukawa da kansa ya yi hatsari ne ranar 25 ga watan Oktoban 2012, a kusa da birnin Yola dake jihar Adamawa.

Bayan ya samu kulawa a asibitoci a birnin Yola da Abuja, sai aka garzaya da shi Jamus da Amurka domin samun karin kulawa.

A wannan lokacin dai jihar da ke arewa maso gabashin Najeriya ta shiga dambarwar siyasa saboda rashin lafiyar gwamnan, kuma bayan ya shafe wata goma yana jinya a kasar waje.

Yusuf Mataima Sule

Hakkin mallakar hoto Kano Government
Image caption Alhaji Yusuf Maitama Sule ya yi gwagwarmaya a fannonin rayuwa da dama

A watan Yuli ne Allah ya yi wa Dan masanin Kano Alhaji Yusuf Maitama Sule rasuwa a wani asibiti da ke kasar Masar. Dan masanin Kano ya mutu yana da shekara 88 a duniya.

Marigayi Maitama Sule shaharraren dan siyasa ne a Najeriya, wanda ya rike mukamin minista a Jamhuriyar ta Farko da kuma jakadan kasar a Majalisar Dinkin Duniya.

A shekarar 1976 ne aka ba shi kwamishinan gwamnatin tarayya mai kula da korafe-korafen jama'a.

Yayin da a shekarar 1979 ya tsaya takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar NPN, sai dai Shehu Shagari ne ya lashe zaben.

Har ila yau, gwamnatin Shagari ta nada shi jakadan Najeriya na dindindin a Majalisar Dinkin Duniya watanni bayan kammala zaben.

A can ne ya jagoranci Kwamitin Musamman kan Yaki da Wariyar Launin Fata na majalisar, wanda masu sharhi ke ganin ba karamin matsayi ba ne.

A shekarar 1957 gabanin Najeriya ta samu 'yancin kanta, marigayi Maitama Sule shi ne ya kewaya da Sarauniyar Ingila Elizabeth yayin da ta kai ziyara Kano yana yi wa jama'a bayaninta.

Ya rasu ya bar 'ya'ya 10 - maza hudu da mata shida.

Alex Ekwueme

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Alex Ekwueme ya zama dattijon da ake tuntuba domin neman shawara bayan ya sauka daga mulki

Tsohon mataimakin shugaban kasar Nigeria, Dr Alex Ifeanyichukwu Ekwueme ya rasu ne a watan Nuwamba a wani asibiti da ke birnin London. Ya rasu ne yana da shekara 85 a duniya.

Marigayin - wanda mai tsara gine -gine ne - ya kasance dan Najeriya na farko da aka zaba a matsayin mataimakin shugaban kasa daga shekarar 1979 zuwa 1983.

Ya fadi ne a gidansa da ke Enugu kuma cikin gaggawa aka tafi da shi wani asibiti da ke birnin Enugu inda ya shiga cikin wani yanayi na doguwar suma.

Daga bisani kuma aka wuce da shi birnin Landan .

Ekweme dai shi ne tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Alhaji Shehu Shagari wanda aka hambarar da gwamnatinsa a juyin mulki da sojoji suka yi a shekarar 1984 a karkashin jagoranci Shugaba Muhamadu Buhari wanda a lokacin Babban Janar ne a rundunar sojin Nigeria.

Kasimu Yero

Hakkin mallakar hoto Whatsapp
Image caption Kasimu Yero gwani ne a fannin wasan kwaikwayo

Shahararren dan wasan kwaikwayon na Hausa, Kasimu Yero, ya rasu a Kaduna a watan Satumba. Marigayin wanda ya rasu yana da shekara 70 ya yi doguwar jinya ne, kamar yadda dansa Mansur Kasimu Yero ya shaida wa BBC. Ya rasu yana da shekara 70 bayan ya yi fama da doguwar jinya.

Alhaji Kasimu Yero ya yi fice ne a shekarun 1980 lokacin da yake fitowa a shirye -shiryen kafar yada labarai ta kasar wato NTA - a wasannin Magana Jari Ce (na Hausa da na Turanci) da Karanbana da dai sauransu.

Sarkin Katagum, Kabir Umar

Hakkin mallakar hoto Family
Image caption Kabir Umar ya rasu bayan ya sha fama da jinya

Sarkin Katagum Alhaji Kabir Umar ya rasu a watan Disamba bayan ya sha fama da jinya. Ya rasu ne a garin Azare jihar Bauchi. Sarkin ya rasu yana da shekara 89.

Ana matukar girmama Alhaji Kabir Umar a masarautar ta Katagum da arewacin Najeriya saboda dattakunsa da rashin tsoma baki cikin harkokin siyasa.

An nada babban dansa, Alhaji Baba Umar Faruk a matsayin sabon Sarkin Katagum.

Gidado Idris

Hakkin mallakar hoto Twitter
Image caption Gidado Idris gogaggen ma'aikacin gwamnati ne

Gidado Idris, wanda ya rasu a watan Disambar nan, gogaggen masanin harkokin mulki ne, ya rike manyan mukamai a Najeriya.

An haifi tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayyar ne a birnin Zazzau a shekarar 1935.

Ya yi karatu a Najeriya da Ingila, kuma ya rike mukamin Sakatare na Musamman ga marigayi Sir Ahmadu Bello, Sardaunan Sokoto.

A wata hira da ya yi da jaridar Daily Trust, ya ce yana cikin mutanen da suka gano gawar Sir Ahmadu Bello bayan an kashe shi a juyin mulkin farko da aka yi a kasar.

Tsohon ministan lafiyar Nigeria Babatunde Osotimehin

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Tsohon ministan lafiya na Najeriya, kuma Babban Darakta a hukumar kula da yawan al'umma ta majalisar dinkin duniya (UNFPA), Farfesa Babatunde Osotimehin ya rasu a watan Yunin 2017, yana da shekara 68.

Marigayin ya mutu ne a birnin New York na Amurka, inda ofishinsa ya ke.

Ya rike mukamin ministan lafiya a lokacin mulkin Marigayi Shugaba Umaru Musa 'Yar'adua daga shekara ta 2007 zuwa 2010.

Mista Osotimehin ya rike mukamai da yawa a ciki da wajen Najeriya, kuma yayi karatu a wasu kasashen waje ciki har da Ingila.

Wazirin Sarkin Musulmin Sokoto, Alhaji Usman Junaidu

Hakkin mallakar hoto Family

Wazirin Sarkin Musulmin Sokoto Alhaji Usman Junaidu ya rasu a ranar 20 ga watan Oktobar 2017.

Marigayi Usman Junaidu dai ya rasu yana da kimanin shekaru 90 a duniya.

Marigayi Usman Junaidu dai ya rasu yana da kimanin shekara 90 a duniya. Ya rasu ne bayan ya yi fama da doguwar jinya a Sakkwaton.

Waziri Usman dai shi ne na 12 a jerin Waziran Sarkin Musulmi da aka yi a tsawon shekara 200 na daular Usmaniyya.

Baya ga wadannan fitattun mutane dai akwai wasu da dama da suka rasa rayukansu, wadanda fitattu ne a wasu fannoni.

Muna fatan Allah ya jikansu ya gafarta musu duka.

Labarai masu alaka