Gwamnati ta musanta kai dan Shugaba Buhari asibitin kasar waje

Yusuf Buhari ya fadi ne a wani mummunar hatsarin babur ranar Talata Hakkin mallakar hoto TWITTER/YUSUF BUHARI
Image caption Yusuf Buhari ya samu karaya ne da rauni a kai a wani mummunar hatsarin babur ranar Talata

Fadar Shugaban Najeriya ta karyata rahoton da ke cewa an fitar da dan Shugaban kasar, Yusuf Buhari kasar waje domin duba lafiyarsa bayan raunin da ya ji sakamakoni hatsarin babur.

Kakakin fadar Shugaban Garba Shehu ne ya shaida wa BBC hakan a lokacin da yake mayar da martani ga wani rahoton da aka wallafa a wata jaridar da ake wallafawa a shafin intanet.

Rahoton dai ya ce an garzaya da Yusuf Buhari wani asibiti a kasar Jamus a wani jirgin daukar marasa lafiya da safiyar Alhamis.

Kazalika rahoton ya ce jirgin ya tashi ne a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja tare da na'urar da ke tallafawa mutum yin numfashi da wani likitan Najeriya.

Sai dai Mallam Garba Shehu ya ce rahoton ba gaskiya ba ne.

Da BBC ta nemi sanin ko akwai shirin fitar da dan shugaban kasar Najeriyar waje, mai magana da yawun shugaban na Najeriya ya ce iyayen matashin ne kawai za su iya yanke wannan shawarar.

Yusuf Buhari ya samu karaya ne da rauni a kai a hatsarin da ya yi a kan babur din tsere ranar Talata.

Labarai masu alaka