Me yake jawo aure-aure barkatai a tsakanin al'ummar Hausawa?
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Adikon Zamani: Me yake sa wasu mazan yawan auri-saki?

Ku latsa alamar lasifikar da ke sama don sauraron shirin tare da Fatima Zahra Umar:

Yayin da wani lokaci zawarawa suka koma abin wasa da dariya, maza kuma da ke 'auri saki' ke yadda suka ga dama ba abin da ya shafe su.

Kusan dai saki ya zama ruwan dare ga maza a arewacin Najeriya, musamman yadda namiji zai yi aure kuma ya saki cikin lokaci kankani.

Irin wadannan mazajen yana da wahala su iya rayuwar aure da mace fiye da shekara daya.

Wasunsu kan saki matarsu bayan haihuwa daya. Suna auren mata su watsar da su yadda suka ga dama.

Ko me ya sa babu wani hukunci a kan irin wadannan mazajen da ke bata rayuwar mata?

Shirin Adikon Zamani na wannan makon ya ci karo da wani magidanci da ya auri mata 13 yana saki, kuma yanzu yake rayuwa da ta 14.

Ya ce bai taba fuskantar kalubale ba wajen neman aure.

Na yi mamakin yadda bai taba fuskantar tirjiya ba daga iyayen matan duk da sun san ya yi kaurin suna a wajen auri-saki.

Wai me ya sa muke barin 'ya'yanmu suna auren irin wadannan mazajen da ke lalata rayuwar mata?

Kuna iya tafka muhawara a shafukanmu na sada zumunta na BBC Hausa Facebook da BBC Hausa Twitter.