Firaministan Mali Idrissa Maiga ya yi murabus

Firaministan Mali Idrissa Maiga mai murabus Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Idrissa Maiga shi ne Firaminista na hudu a gwamnatin Keita

Firaministan Mali Idrissa Maiga ya yi murabus tare da gwamnatinsa, kamar yadda fadar gwamnatin kasar ta sanar.

Sanarwar da fadar shugaban kasar ta fitar ta ce Firaministan ya gabatar da takardar murabus din ne ga shugaba Ibrahim Boubakar Keita.

Kuma sanarwar ta ce Maiga ya yi murabus ne tare da gwamnatinsa.

A watan Afrilu ne aka nada Idrissa Maiga matsayin Firaminista.

Maiga shi ne Firaminista na hudu a gwamnatin Keita, bayan gwamnatin Omar Tatam Ly da Moussa Mara da Modibo Keita.

Murabus dinsa na zuwa ne a yayin da ya rage watanni bakwai a gudanar da zaben shugaban kasa wanda za a gudanar a watan Yulin 2018.

Maiga shi ne mataimakin shugaban jam'iyyar RPM mai mulki a Mali, kuma ya taba zama daraktan yakin neman zaben Shugaba Keita a zaben 2013.

Sai dai kuma babu wani cikakken bayani a sanarwar da gwamnatin ta fitar game da dalilin murabus din Firaministan.

Labarai masu alaka