'Sojojin Nigeria sun fatattaki 'yan Boko Haram daga Kanamma'

Sojin Najeriya masu yaki da kungiyar Boko Haram Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Sojin Najeriya sun ce sun fatattaki 'yan Boko Haram daga yankin

Rundunar sojan Najeriya ta ce ta fattaki mahara da ake zargin 'yan Boko Haram ne da suka kai hari a wani barikin soja da ke garin Kanamma a jihar Yobe.

Rahotanni sun kuma bayyana cewa maharan sun yi hakon wasu kauyuka a yankin wanda suke kusa da iyakar Najeriya da Nijar.

To sai dai kwamandan rundunar dake yaki da Boko Haram ta Operation Lafiya Dole, Manjo Janar Nicholas Rogers ya shaida wa BBC cewa sojoji na sama da na kasa sun kori 'yan Boko Haram din.

Ya kara da cewa jami'an tsaro sun yi amfani da jirgin saman yaki a lokacin artabun wanda aka dauki lokaci mai tsawo ana yinsa.

To amma ya ce kawo yanzu ba zai iya tabbatar da irin hasarar rayuka ko jikkata da aka yi a lamarin ba.

A halin da ake ciki kuma wasu rahotanni na cewa wasu mahara da ake jin 'yan Boko Haram ne sun kai hari a kauyen Maiwa dake kusa da Maiduguri babban birnin jihar Borno inda suka kashe akalla mutane hudu.

Bayanai sun ce wadanda lamarin ya rutsa da su a jiya Asabar sun tafi daji ne domin nemo icen hura wuta.

Kwamandan rundunar ta yaki da Boko Haram ya nanata kira ga mayakan Boko Haram yana cewa su tuba su ajiye makamansu. Ya ce duk wanda ya ajiye makaminsa kuma ya tuba, to rundunar soja ba zata yake shi ba.

Labarai masu alaka