Buhari zai shimfida layin dogo daga Kano zuwa Maradi

Jawabin shugaba Buhari na sabuwar shekara ya mayar da hankali ne kan samar da ababaen more rayuwa Hakkin mallakar hoto NIGERIAN GOVERNMENT
Image caption Jawabin shugaba Buhari na sabuwar shekara ya mayar da hankali ne kan samar da ababaen more rayuwa

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce an yi nisa da tattaunawa kan gina hanyar jirgin kasa daga Kanon Najeriya zuwa Maradin Nijar.

Shugaban da ya bayyana hakan a wani jawabin sabuwar shekarar da ya yi wa 'yan kasar, inda ya ce layin dogon zai ratsa ta Kazaure da Daura da Katsina da Jibiya har zuwa Maradin.

Shugaban ya kuma ce an fara gina wani layin dogon daga Legas zuwa Kano kuma layin zai kai Ibadan zuwa karshen shekarar 2019.

Ya ce layin zai dinga jigilar mutum miliyan biyu da kuma kaya tan miliyan biyar a ko wacce shekara tsakanin Legas da Ibadan.

Ya ce shi ya rattaba hannu kan aikin gina layin dogo daga Fatakwal zuwa Maiduguri kuma layin zai ratsa Aba da Owerri da Umuahia da Enugu da Awka da Abakaliki da Makurdi da Lafia da Jos da Bauchi da Gombe da Yola da kuma Damaturu.

Ya ce game da kammala hanyar jirgin kasa ta cikin birnin Abuja kuwa, tuni an kai ga kashi 98 cikin 100, kuma jirgin kansan zai fara aiki ne bayan an gwada shi.

Shugaba Buhari ya ce jirgin kasan Abuja zai tallafa wa harkar kasuwanci a babban birnin tarayyar Najeriyar.