Manoma 700 sun tsere daga hannun Boko Haram — Sojoji

Sojoji na tantance mutanen domin su kay masu tayar da kayar baya su samu damar sulalewa cikin gari Hakkin mallakar hoto NIGERIAN ARMY
Image caption Sojoji na tantance mutanen domin su kay masu tayar da kayar baya su samu damar sulalewa cikin gari

Rundunar sojin Najeriya ta ce sama da manoma da masunta 700 suka tsere daga hannun 'yan Boko Haram daga tafkin Chadi zuwa Monguno.

Wata sanarwar da Kanar Timothy Antigha na runduna ta takwas ta sojin Najeriya ya sanya wa hannu, ta ce tserewar mutanen da a da suna hannun 'yan Boko Haram ne ba ya rasa nasaba da samamen da sojojin kasar suka kai cikin 'yan kwanakin nan.

Kanar Timothy ya ce an kai samamen ne bayan nasarorin da sojojin suka samu a hare-haren da suka kai garin Chikun Gudu da wasu kauyukan da ke kusa da shi.

Sanarwar dai ta ce manoman da masuntan da kuma iyalansu sun samu tarbar bataliya ta 242 a Monguno, inda ake kan tantance su domin gudun kar wani mai tayar da kayar baya da ka iya kasancewa a cikinsu ya yi amfani da damar ya sulale cikin gari.

Ta kuma ce mata biyu masu juna biyu sun haihu a sansanin da sojojin suka ajiye mutanen.

Hakkin mallakar hoto NIGERIAN ARMY
Image caption Rundunar sojin Najeriyar ta ce masunta da manoman dai sun tsere ne da iyalansu

Kanar Timothy Antigha ya ce a halin yanzu sojojin sun mayar da hankali ne kan sanin inda kwamamdojin Boko Haram da sojin ke nema suka koma.

Kanar Antigha ya ce sojojin da suka kai samamen sun hada da sojojin sama da kuma sojojin kasa masu amfani da manyan makamai, kuma sun yi nasarar lalata abubuwan da masu tayar da kayara bayan Boko Haram ke amfani da su wajen sadarwa da kere-kere da kayayyakin hada bama-bamai da motoci da sauransu.

Rundunar ta ce lalata abubuwan da 'yan Boko Haram din ke amfani da su da kuma abubuwan da rayuwarsu ta ta'allaka akai shi ya sa suka tsere suka bar mutanen da suka kama.

Wannan na zuwa ne a lokacin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yake nanata cewa gwamnatinsa ta ci galaba a kan Boko Haram.

Hakkin mallakar hoto NIGERIAN ARMY
Image caption Rundunar sojin ta ce a cikin wadanad suka tsere daga 'yan Boko Haram din mata biyu masu juna biyu sun haihu

Labarai masu alaka