Mutum 10 sun mutu a zanga-zangar Iran

Mutum 10 sun mutu a zanga-zangar Iran Hakkin mallakar hoto STR
Image caption Mutum 10 sun mutu a zanga-zangar Iran

A cewar kafar talbijin din kasar, mutum 10 ne suka mutu a daren jiya, a zanga-zangar nuna adawa da gwamnati a Iran.

Ta kara da cewa, "Abin takaici kimamin mutum 10 ne suka mutu a birane da dama".

Zuwa yanzu dai a kalla mutum 12 ne suka mutu tun daga lokacin da aka fara zanga-zangar ranar Alhamis.

A ranar Litinin ne Shugaba Hassan Rouhani ya ce yin zanga-zanga da yin suka duka samun dama ne, ba barazana ba.

Ya ce gwamnatin kasar za ta hada hannu da 'yan kasar ta yi aiki don fitar da kasar daga matsin tattalin arzikin da take fuskanta.

A baya shugaban ya sha fadar cewa 'yan kasar na da damar yin zanga-zanga, amma ba ta hanyar yin tashin hankali ba.

Ko da yake an ci gaba da yin zanga-zangar.

'Yan sanda sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye don tarwatsa gangamin a dandalin Tehran's Engheleb.

An kuma samu rahoton cewa an samu barkewar zanga-zanga a Kermanshah da Khorramabad da ke yammacin kasar, da Shahinshahr a arewa maso yammacin kasar da kuma arewacin birnin Zanjan.

Gidan talbijin din kasar ya ce masu zanga-zangar sun yi kokarin kwace wasu ofisoshin 'yan sanda da sansanonin soji, sai dai sun fuskanci matsanancin matsin lamba daga dakarun tsaro.

Yaushe aka fara zanga-zangar?

An kira zanga-zangar wadda aka fara ta a ranar 30 ga watan Disambar 2017 ce ta kafofin sadarwa na intanet, duk da gwamnati ta yi kashedin shirya duk wani gangamin da ya sabawa doka.

Wasu hotunan bidiyo da aka yada a shafukan sadarwa na intanet sun nuna yadda masu zanga-zangar ke arangama da masu zanga-zanga.

Masu zanga-zangar na adawa ne da gazawar gwamnatin shugaba Hassan Rouhani kan magance matsalar hauhawan farashin kayayyakin masarufi.

Zanga-zangar ta rikide ta koma ta adawa da gwamnati tare da yin kiran a saki fursunonin siyasa da kawo karshen cin zarafin da 'yan sanda ke yi wa jama'a.

Masharhanta a gabas ta tsakiya sun ce zanga-zangar ta zo wa gwamnatin Iran ba-zata, wacce ba a saba gani ba.

Wani sakamakon binciken BBC game da Iran ya nuna cewa kashi kusan 30 na 'yan kasar na shiga hali na talauci a shekaru 10 da suka gabata.

Wasu na ganin kudaden ya kamata a ce an kashe domin inganta rayuwarsu, amma an koma ana hidimar yaki da kudaden a Syria da Yemen da Iraqi.

Sannan ana kashe makudan biliyoyi domin watsa farfagandar shi'a a sassan duniya

Shugaba Hassan Rouhani ya yi alkawalin cewa yarjejeniyar nukiliya da ya sanya wa hannu tsakanin Iran da manyan kasashen duniya za ta taimaka wajen farfado da tattalin arzikin kasar idan har an cire ma ta takunkumai.

Tattalin arzikin kasar dai yanzu ya fara bunkasa kamar yadda aka samu sassauci a hauhawan farashin kayayyaki amma har yanzu kasar na fama da karancin masu saka jari yayin da alkalumman rashin aikin ya kai kashi 12.4.

Hassan Rouhanii

Labarai masu alaka