Nigeria: An kashe mutum 21 a jihar Rivers

Rundunar 'yan sandan jihar Rivers dai ta tabbatar da abkuwar lamarin. Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Rundunar 'yan sandan jihar Rivers dai ta tabbatar da abkuwar lamarin.

Wasu 'yan bindiga sun kashe mutum 21 bayan sun fito daga coci don addu'o'in murnar sabuwar shekara a jihar Rivers da ke yankin kudu maso kudancin Nigeria.

Lamarin ya abku ne a garin Omoku da ke karamar hukumar Ogba-Egbema-Ndoni mai nisan kilomita 85 daga birnin Porthacourt.

Rundunar 'yan sandan jihar dai ta tabbatar da abkuwar lamarin.

Kawo yanzu dai babu cikakken bayani kan wadanda suka kai harin.

Sai dai wasu rahotanni na cewa harin yana da nasaba da rigingimu da ake yi tsakanin wasu gungu da basa ga maciji da juna a yankin Naija Delta mai arzikin man fetur.

Wannan hari dai na zuwa bayan kashe wani basaraken gargajiya na Masarautar Numana wato Etum Numana, Dr Gambo Makama a karamar hukumar Sanga da ke kudancin jihar Kaduna.

Rundunar 'yan sandan jahar ta tabbatar da afkuwar al'amarin, sai dai ta ce kawo yanzu ba ta sami nasarar cafke ko da daya daga cikin maharan ba.

A na ta bangaren gwamnatin jihar Kaduna ta yi alla-wadai da kisan da ta ce kokari ne wasu da ke yi na neman wargaza zaman lafiyar da al'ummar jihar ke ciki.

Labarai masu alaka