Isra'ila ta bai wa 'yan Afirka wa'adin kwana 90 su bar kasar ko a daure su

african migrants in israel Hakkin mallakar hoto Getty Images

Isra'ila ta bai wa dubban bakin haure 'yan Afirka wa'adin kwana 90, da su fice daga kasar ko kuma su fuskanci dauri a gidan maza.

Wasu mutum 38,000 sun fadi jarrabawar neman mafaka, mafi yawansu kuma 'yan kasar Eritiriya da Sudan ne.

A yanzu sai dai su koma gida ko su tafi Yuganda ko Ruwanda, kuma an bai wa ko wannensu taimakon kudi dala 3500, don su kama hanya.

Sai dai wannan umarni ya ware yara kanana da tsofaffi da wadanda suka kubuta daga kangin bauta da na safarar mutane.

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya da kungiyoyin kare hakkin bil adama, sun ce kawar da 'yan bakin hauren ya saba wa dokar kasa da kasa.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Labarai masu alaka