Gwamnan tsohuwar Jihar Kaduna Lawal Kaita ya rasu

Hakkin mallakar hoto Jami'ar Al Qalam Katsina
Image caption Alhaji Lawal Kaita jinin sarautar Katsina ne

Gwamnan tsohuwar Jihar Kaduna Alhaji Lawal Kaita ya rasu bayan fama da rashin lafiya.

Rahotanni sun ce fitaccen dan siyasar a Najeriya, ya rasu ne a yau Talata a wata asibiti a birnin Tarayya Abuja.

Tsohon gwamnan ya rasu yana da shekaru tamanin da biyar a duniya.

Kaita ya yi gwamna ne a inuwar jam'iyar NPN a tsohuwar jihar Kaduna a 1983 kafin sojoji su yi wa Shagari juyin mulki.

Labarai masu alaka