Nigeria: An kashe mutum goma a masallacin Gamboru

A ranar Talata ne dai shugaban wani bangare na Boko Haram, Abubakar Shekau ya fitar da wani bidiyo inda ya yi barazanar kaddamar da wasu hare-hare Hakkin mallakar hoto .
Image caption A ranar Talata ne dai shugaban wani bangare na Boko Haram, Abubakar Shekau ya fitar da wani bidiyo inda ya yi barazanar kaddamar da wasu hare-hare

Wani dan kunar bakin wake ya kai hari wani masallaci a garin Gamboru da ke jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya.

Dan kunar bakin waken ya badda kama ne ya shiga cikin masallaci.

Ya tayar da bam dinsa a lokacin da ake sallar Asuba.

Shaidu sun tabbatar wa BBC cewar harin ya kashe mutum goma ciki har da maharin.

Kawo yanzu dai babu wanda ya dauki alhakin kai wannan harin.

Sai dai kuma shugaban wani bangare na kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau, ya yi barazanar kai wasu hare-hare a wani bidiyon da ya fitar ranar Talata.

Kwanakin nan ne dai shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya nanata cewar dakarun Najeriya sun sami galaba a kan mayakan Boko Haram duk da cewar 'yan kungiyar suna kai hare-haren kunar bakin wake.

Labarai masu alaka