Makunnin nukiliyata ya fi na Kim Jong-Un — Trump

Donald Trump Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaban Amurka da na Koriya ta arewa sun koma suna cacar-baki tsakaninsu.

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce makunnin nukiliyarsa ya fi girma da karfi fiye da na shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong-un.

Wannan dai ci gaban cacar-baki ne tsakanin shugabannin kasashen biyu da ke wa juna barazanar makaman nukiliya.

Mista Trump ya mayar da martani ne ga kalaman da Mista Kim ya yi kan cewa makunnin nukiliyarsa yana kan teburinsa.

Martanin na Trump dai ya ja hankali musamman a shafukan sada zumunta na intanet.

Wannan na cikin jerin sakwannin da Trump ya wallafa a twitter a kwanan nan, inda ya sanar da lambar yabo ga gurbatattun kafafen yada labarai da kuma barazanar janye tallafi ga Falasdinawa saboda abin da ya kira rashin nuna godiya da mutuntawa.

A cikin sakwannin kuma ya yabi kansa inda ya ce zamaninsa an samu karancin hatsarin jiragen sama.

Masharhanta dai na ganin zabin kalaman shugabannin biyu wani salo ne na diflomasiya tsakaninsu.

"Ina ganin shugaban ya dauki wannan kamar wani abin nuna karfi ne," Kamar yadda Jim Himes dan majalisar dokoki a jam'iyyar democrat ya shaidawa CNN.

Eliot A Cohen, tsohon mai ba Condoleezza Rice shawara ya ce akwai yarinta a sakon Trump, duk da cewa kuma kalamansa sun yi muni.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaban Koriya ta arewa Kim Jong-un ya ce makunnin nukiliyarsa yana kan teburinsa.

Mutane da dama sun bukaci kamfanin twitter ya toshe duk wani sakon da ke kiran "yakin nukiliya" tare da haramta yada bayanin a shafinsa.

Sai dai magoya bayan Trump sun kare shi, suna masu cewa kalaman shugaban sun yi daidai domin ya nuna karfin Amurka.

Ko Trump zai iya danna makunnin?

Shugaban Amurka dai yana da iko da makunnin nukiliya.

Sai dai hanyoyin kaddamar da harin nukiliyar ba ya wani bukatar danna wani makunni.

Bayan doguwar tuntuba, dole sai shugaban ya mika lambobin nukiliyar ga manyan jami'an soji. An buga lambobin ne a wani kati da ake kira "biscuit", wanda ke hannun shugaban a kullum.

Ko Koriya ta arewa za ta iya danna makunninta?

Koriya ta arewa na ikirarin tana da makamin nukiliya da za ta iya kai wa Amurka hari, amma duk da masana sun amince Pyongyang tana da makamin nukiliya, amma babu tabbas ko ta mallaki fasahar da za ta iya amfani da shi idan bukatar ta taso.

Labarai masu alaka

Karin bayani