Za a ba da tukwicin miliyan 200 ga wanda ya gano maharan Rivers

Nyesom Wike Hakkin mallakar hoto Nyesom Wike Twitter
Image caption Gwamna Wike ya ce ba za a amince da kara faruwar irin wannan tashin hankalin ba

Gwamnan jihar Rivers da ke kudancin Najeriya ya yi alkawarin bayar da tukwicin naira miliyan 200 ga duk wanda ya bayar da bayanan da za su sa a kama 'yan bindigar da suka hallaka mutum 16 a ranar farko sabuwar shekarar 2018.

Mutanen da aka kashe din dai na kan hanyarsu ne ta dawowa daga coci da safiyar ranar Litinin din.

Gwamna Nyesom Wike ya kara da cewa gwamnati za ta kwace kadarorin duk wanda aka kama da hannu a kisan da aka yi a garin Omuku din.

Ya kuma ce, "ba za mu amince da kara faruwar irin wannan tashin hankalin ba.

"Mun umarci hukumomin tsaro da su tabbatar sun yi maganin maharan. Na yi bakin cikin faruwar wannan abu matuka, ya isa haka."

Ana danganta wannan lamari ne da karuwar tashin hankalin da ake samu tsakanin kungiyoyin da ba sa ga-maciji da juba a jihar mai arzikin man fetur, bayan da wani shirin afuwa da gwamnati ta yi ya zo karshe.

Gwamnatin tsohon Shugaba Goodluck Jonathan ce ta gabatar da shirin afuwar, wanda ya kawo dan zaman lafiya a yankin.

A da can baya dai yankin ya sha fama da hare-haren masu tayar da kayar baya, da suke neman a dinga ba su rabo mai tsoka da ya fi na ko wanne yanki daga arzikin man fetur din Najeriyar.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Jihar Rivers na yawan fama da rikicin masu tayar da kayar baya

Labarai masu alaka