An sace Basaraken Zangon Kataf a Kaduna

An sace Basarake a Kaduna Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Jihar Kaduna na daga cikin sassan da suka fi fama da sace-sacen mutane

'Yan bindiga sun sace Sarkin garin Ikulu Yohanna Kukah da ke karamar hukumar Zangon Kataf a Jihar Kaduna.

Rahotanni sun ce an sace Sarkin ne da safiyar yau Laraba.

Wata majiya ta ce 'yan bindigar sun abka fadar Sarkin ne suka yi awon gaba da shi ba tare da sun bukaci wani abu daga iyalan shi ba.

Rundunar 'yan sandan Jihar Kaduna ta tabbatar da aukuwar lamarin, inda ta ce ta samu labarin bayan an sace Sarkin da safe.

Sarkin dai dan uwa ne ga babban malamin darikar katolika a Najeriya Bishop Mathew Kukah.

Wannan na zuwa bayan wasu 'yan bindiga sun hallaka Sarkin Lumana dakta Gambo Makama tare da matarsa Ruth mai dauke da juna biyu, a kauyensu mai suna 'Arak' da ke karamar hukumar Sanga a jihar Kaduna.

Jihar Kaduna dai na daga cikin sassan da suka fi fama da sace-sacen mutane don neman kudin fansa a Najeriya.

Labarai masu alaka