Dambarwar China da Taiwan ta koma kan jami'o'i

Dalibai da masu rajin kare 'yancin Taiwan na zanga-zangar abin da suka kira alamar dogaro ga arzikin China Hakkin mallakar hoto ASSOCIATED PRESS
Image caption Taiwan na zargin China ce take aikewa da wasikun da ba a san daga inda suka fito ba masu sukan lamirin jami'o'in Taiwan din

Jami'an gwamnatin Taiwan sun kare jami'o'in kasar bayan da aka aike da wasu wasiku da ba a san daga inda suka samo asali ba zuwa ga makarantu daban-daban a Malaysia, inda a cikin wasikun ake shawartar iyaye da su guji tura 'ya'yansu makarantun Taiwan.

Jami'an Taiwan din dai sun sheda wa BBC cewa lamarin ba zai rasa nasaba da siyasa ba.

China dai har kullum tana daukar tsibirin na Taiwan a matsayin wani bangare na kasarta, wanda ko ba dade ko ba jima take ganin zai dawo karkashin ikonta.

Shekara daya ke nan da China take ta kara matsa lamba a kan Taiwan din tun bayan da sabon shugaban Taiwan din ya ki amincewa ya yarda kasar tasa wani bangare ne na China.

An aika da wasikun ne zuwa ga wasu daga cikin manyan makarantu 60 na Malaysia wadanda daliban China ke karatu a cikinsu, inda a cikin wasikun ake gaya wa iyaye cewa za su lalata rayuwar 'ya'yansu idan suna tura 'ya'yan nasu jami'o'in Taiwan.

A cikin wasikun an rika bayyana illolin da aka ce suna tattare da yin karatu a Taiwan tare kuma da nuna irin alfanun da ke cikin karatu a China.

Wani jami'in gwamnatin Taiwan ya sheda wa BBC cewa mai yuwuwa ne an turo wasikun ne bisa umarnin gwamnatin China.

Dangantaka tsakanin China da Taiwan ta yi tsami tun 2016 lokacin da Taiwan din ta zabi sabon shugabanci mai ra'ayin samun 'yanci daga China.

Sakamakon dangantakar da ta yi tsami tsakanin bangarorin biyu, 'yan kalilan din daliban China ne ke zuwa Taiwan karatu, duk da cewa jami'o'in Taiwan din na da matukar burin samun dalibai daga kasashen waje.

Sai dai jami'an gwamnatin Taiwan sun ce ba su da wata fargaba kan ko wasikun za su hana daliban Malaysia zuwa makarantun nasu, suna masu jaddada cewa makarantun Taiwan na bayar da ilimi mai nagarta kuma cikin sauki.

Ana dai samun dalibai da dama daga Malaysia da kuma wasu kasashe na Kudu-maso-gabashin Asia da ke son zuwa karatu a Taiwan a shekarun nan, kasancewar kasar na kan tsari na mulkin dumokuradiyya da kuma kasancewarta mai al'adu na China.

Sai dai kuma duk da haka China ta fi jan daliban kasashen waje fiye da ita Taiwan din