Trump ya rushe hukumarsa ta binciken magudin zabe

Shugaba Donald Trump Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Fadar gwamnatin Amurka ta ce yawancin jihohin kasar sun ki ba wa hukumar hadin kai

Fadar gwamnatin Amurka, White House ta ce Shugaba Donald Trump ya rushe hukumar da ya kafa domin gudanar da bincike kan magudin zabe da ya yi zargin ana yi a lokacin zaben shugaban kasa na 2016.

A watan mayu na shekarar da ta kare ne shugaban ya kafa hukumar bayar da shawara a kan tabbatar da gaskiya a zabe.

A lokacin da shugaba Donald Trump ya kafa hukumar ya bayar da tarin bayanai na magudin zabe da yake zargi ana yi, inda ya ce har kusan mutane miliyan uku ne suka kada kuria a zaben shugaban kasar na 2016, ba bisa ka'ida ba.

A karshe dai Mista Trump ya yi nasara a zaben da yawan wakilai, abin da ya kai shi ga darewa a kujerar mulkin kasar, yayin da abokiyar karawarsa a zaben Hillary Clinton ta jam'iyyar Democrat wadda ta fi shi yawan tsantsar kuri'a ta sha kaye.

A da dai shugaban ya ce Clinton ta fi shi yawan kuriu ne saboda saboda miliyoyin kuriun da ya yi zargin ana kadawa ba bisa ka'ida ba.

To amma a gaba dayan jihohin kasar ta Amurka ba wata jiha da ta samu wata gagarumar sheda da za ta tabbatar da zargin na Shugaba Trump.

A don haka yanzu ya yanke shawarar rushe hukumar, kamar yadda ya ce maimakon ya ci gaba da dambarwar shari'un da ba za su kare ba da kudin jama'a.