An dakatar da masu tukin jirgin saman da suka yi fada a cikin jirgi

A Jet Airways flight Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Jirgin, wanda ke dauke da fasinja 324, ya sauka a Mumbai ba tare da wata matsala ba.

Kamfanin jirgin sama na Jet Airways ya dakatar da masu tukin jirginsa biyu bayan wasu rahotanni sun nuna cewa sun yi fada a dakin da ake tuka jirgin lokacin da suke kan hanya daga London zuwa Mumbai.

Kamfanin jirgin ya ce an samu "rashin jituwa" tsakanin matuka jirgin ne ranar farko ta wannan shekarar.

Yakara da cewa an dakatar da matuka jirgin ne har sai an kammala bincike kan lamarin.

Jirgin, wanda ke dauke da fasinja 324, ya sauka a Mumbai ba tare da wata matsala ba.

Rahotannin da kafafen watsa labarai suka bayar sun ambato ganau na cewa lamarin ya faru ne bayan wani matukin jirgi ya mari takwararsa.

Matukiyar ta fice daga dakin tukin jirgin ko da yake ta koma daga baya.

Mai magana da yawun kamfanin Jet Airways ya tabbatar wa BBC aukuwar lamarin, sai dai bai yi cikakken bayani ba.

Kamfanin ya ce ya shaida wa hukumar kula da sufurin jiragen sama aukuwar lamarin, yana mai cewa ba zai bari wani ma'aikacinsa ya kawo cikas kan tsaro da lafiyar jirgin ba.

Labarai masu alaka