Buhari ya bude tashar ruwa ta kan tudu ta farko a Nigeria

Dubban mutane za su samu aiki
Image caption Dubban mutane za su samu aiki

Shugaban Nigeria Muhammadu Buhari ya kaddamar da tashar ruwa ta kan tudu ta farko a kasar a birnin Kaduna da ke arewacin kasar.

An hada tashar ne da titin jirgin kasa daga babbar tashar ruwa a Lagos zuwa arewacin kasar.

Shugaban ya ce "masu yin kasuwanci a kan tudu sun jima suna jiran bude irin wannan tasha wacce za ta saukaka yadda ake kasuwanci".

An kiyasta cewa za ta dauki kusan ton dubu talatin na kago a shekara, kuma za ta kasance cibiyar rarraba kayayyaki a arewacin kasar har ma watakila zuwa Nijar da Chadi.

Gwamnatin Nigeria dai na fatan bude wasu karin tasoshin ruwan na kan tudu guda shida a Ibadan, Aba, Kano, Jos, Funtua da Maiduguri.

Image caption Wannan ita ce tasha ta farko a Najeriya

Labarai masu alaka