Sojojin Nigeria sun sake gano wata 'yar Chibok

Har yanzu akwai ragowar 'yan matan Chibok da ba a gano ba Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Har yanzu akwai ragowar 'yan matan Chibok da ba a gano ba

Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta sun sake gano daya daga cikin 'yan matan Chibok da mayakan Boko Haram suka sace a shekarar 2014.

Manjo Janar Rogers Ibeh Nicholas, kwamandan rundunar samar da zaman lafiya ta Operation Lafiya Dole, ya tabbatarwa BBC cewa an gano yarinyar ne ranar Alhamis da safe.

Wata sanarwa da mataimakin daraktan hulda da manema labara na rundunar Kanal Onyema Nwachukwu ya fitar ta ce an gano yarinyar ne a garin Pulka da ke jihar Borno.

A cewar sanarwar, "Zuwa yanzu, kwarya-kwaryar binciken da aka yi ya nuna cewa yarinyar, mai suna Salomi Pagu ita ce ta 86 cikin jerin 'yan matan Chibok da aka sace wadanda aka wallafa sunayensu a shafin intanet".

A lokacin da aka gano ta tana tare da wata yarinya mai suna Jamila Adams, mai kimanin shekara 14 da kuma wani jariri kuma yanzu haka sojoji suna kulawa da su tare da ba su magunguna, in ji sanarwar.

Wannan ne karon farko da aka gano wata 'yar Chibok tun bayan wadanda aka sako a watan Mayun shekarar 2017.

A wancan lokacin, 'yan matan sun gana da Shugaba Muhammadu Buhari sa'o'i kadan kafin tafiyarsa jinya Birtaniya.

Labarai masu alaka