Daraktoci suna son kai wajen zabar wanda zai yi fim — Ciroki

Daraktoci suna son kai wajen zabar wanda zai yi fim — Ciroki

Daya daga cikin `yan wasan farko da suka shahara a masana'antar fina-finan Hausa ta Kannywood a Najeriya, wato Bashir Bala, wanda aka fi sani da Chiroki ya sake komawa dandamali bayan lokaci mai tsawo ba a jin duriyarsa.

Chiroki dai ya yi kaurin suna a fagen barkwanci da shirya munafunci, kuma rawar da ya taka kenan a cikin wani sabon fim mai suna juyin-sarauta.

Ibrahim Isa ya tambaye shi abin da ya sa ba ya fitowa sosai a fina-finan Kannywood:

"Ina nan ba buya na yi ba. Ka san shi wasa, ko kuma in ce fim, ba mutum shi yake daukar kansa ya jefa inda yake so ba.

"Akwai masu bayar da umarni, kamar abin da ake nufi koci a filin ball. Toh su ne suke da ra'ayin idan sun shirya fim, su dauko ka su sa ka.

"Yauwa. To ko ka iya ko baka iya ba , akwai wani ra'ayi nasu, da masu bayar da umarni da masu shirya fim, za a iya daukar ka a ajiye ka a kan benci sai bal ta zo karshe, mai yiwuwa in Allah Ya taimake ka sai a tuna wannan bal din fa babu wanda zai iya cin ta sai wane. Sai a dauko ka sai a saka.

"Misali zan maka. Ai mutane suna ganin kaman ba ma nan, ko kuma a'a mun ja baya ne kokuma yanzu ba mu iya ba.

"Toh salo ne da taku ya sauya na harkar wasanni. Na farko akwai jari hujja. Duk aktan da ka ga ana yawan ganinsa yana da jari ne a hannunsa.

"Zai iya fim nasa na kansa. Toh ka ga wannan ba za a iya cewa ya yi 'difom' ko kuma a'a basiarasa ta kare an daina yayinsa ba. A'a. Ba a daina yayin dan wasa ko wane iri ne.

"Sai dai idan daraktas ba sa ra'ayinsa za su iya ajiye shi, sai lokacin kuma da suka ga tunaninsu ya dawo kanka.

"Kamar yanzu Hajiya Balaraba Ramat Mohammed tana daya daga cikin wadanda suke kokartawa manyan aktoci da ake ajiyewa, ta shirya wani fim.

"Toh, role din da ma ta yi niyyar ba ni, ba shi aka ba ni ba daga farko, amma daga karshe sai aka zo aka zauna aka ga a 'to ai akwai munfunci a fim din, tun da ga Ciroki ya kware a wajen, a zo a gwada shi mana."