Salah da Asisat Oshoala sun zama gwarzayen CAF na 2017

Mohamed Salah Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Mohamed Salah ya ci wa Liverpool kwallo 17 a Premier bana

Dan wasan gaba na Liverpool da Masar Mohamed Salah ya zama gwarzon dan kwallon kafa na hukumar kwallon kafa ta Afirka, CAF na shekara ta 2017.

Dan wasan mai shekara 25, wanda ya ci kwallo 17 a gasar Premier ta bana, ya taimaka wa kasarsa Masar ta samu gurbin gasar cin kofin duniya da kuma zuwa wasan karshe na gasar cin kofin Afirka a 2017.

Salah, wanda shi ne daman ya zama gwarzon dan kwallon Afirka na shekara na BBC a watan Disamba, ya doke abokin wasansa ne a kungiyar Liverpool Sadio Mane a gasar ta CAF.

Salah da Mane sun halarci bikin bayar da kyautar a Accra, babban birnin Ghana, sa'a 24 kafin wasan da kungiyarsu za ta yi na cin kofin FA, ranar Juma'a da Everton, wasan da Salah ba zai buga ba saboda rauni.

Dan wasan gaba na kungiyar Borussia Dortmund da Gabon Pierre-Emerick Aubameyang shi ne ya zo na uku.

A farkon shekarar da ta kare ta 2017, dan wasan na Masar ya taka muhimmiyar rawa a lokacin da kasar tasa ta zama ta biyu a gasar cin kofin kasashen Afirka.

Haka kuma ya taimaka wajen cin dukkanin kwallo bakwai da Masar ta ci, da suka ba ta damar samun gurbin zuwa gasar kofin duniya a karon farko tun shekara ta 1990, inda ya bayar aka ci biyu, shi kuma ya ci biyar, ciki har da fanaretin daidai lokacin tashi wadda ya ci Congo suka samu gurbin gasar ta duniya wadda za a yi a Rasha.

Salah ya yi kokari a matakin kungiya kamar yadda yake yi a tawagar kasarsa.

A Italiya ya ci kwallo 15 kuma ya taimaka aka ci 11, inda ya taimaka wa Roma ta zama ta biyu a teburin gasar Serie A, kafin ya koma Liverpool, inda a nan kuma a bana ya ci 23 a wasa 29 zuwa yanzu.

A bangaren mata 'yar wasan Najeriya kuma tsohuwar 'yar kungiyar mata ta Arsenal Asisat Oshoala ita ce ta ci kyautar ta gwarzuwar 'yar kwallon kafa ta nahiyar ta Afirka ta shekara ta hukumar ta CAF.

Hakkin mallakar hoto Kevin C.Cox
Image caption 'Yar wasan Najeriya kuma tsohuwar 'yar kungiyar Arsenal ta mata Asisat Oshoala ta ci kyautar ne a karo na biyu

'Yar kwallon mai shekara 22, da ta ci kyautar a karo na biyu wadda ke cike da shaukin wannan nasara ta shawarci matasan 'yan kwallo mata da su yi koyi da irinta kamar yadda ta cimma burinta.

Kungiyoyin kwallon kafa da dama da sauran masu ruwa da tsaki a harkar kwallon kafa sun samu lambobin bajintarsu daban daban, ciki har da tsohon gwarzon dan kwallon kafa na duniya da kuma Afirka, a yankuma sabon zababben shugaban kasar Liberia, mai jiran gado George Weah.

A wannan shekara dai hukumar kwallon kafar ta Afirka , CAF, ta daina bayar da kyautar gwarzon dan kwallon kafa na Afirka mai taka leda a cikin nahiyar da kuma lambar gwarzon alkalin wasa na shekara, a bisa tsarinta na tabbatar da martabar wasan a Afirka.

Wannan ne karon farko da aka ba wa jama'a dama su kada kuri'a a zaben gwarzon dan kwallon kafar na Afirka na shekara, wanda a da masu horad da tawagogin kwallon kafa na kasashen Afirka da kuma kyafti-kyaftin na tawagogin ne ke zaben.